Saudiyya ta zartar wa mutum 4 hukuncin kisa
A shekaran jiya Laraba ne hukumomi a kasar Saudiyya suka zartar da hukuncin kisa a kan mutane hudu ranar Laraba.Uku daga cikin mutanen ‘yan kasar ne da aka samu da laifin kisan kai; na hudu kuma dan kasar Siriya ne da aka samu da laifin safarar miyagun kwayoyi.Daga farkon wannan shekarar zuwa yanzu, an yanke […]
A shekaran jiya Laraba ne hukumomi a kasar Saudiyya suka zartar da hukuncin kisa a kan mutane hudu ranar Laraba.
Uku daga cikin mutanen ‘yan kasar ne da aka samu da laifin kisan kai; na hudu kuma dan kasar Siriya ne da aka samu da laifin safarar miyagun kwayoyi.
Daga farkon wannan shekarar zuwa yanzu, an yanke hukuncin kisa a kan mutane 130 as kasar, lamarin da ke nuna karuwar wadanda ake yanke wa hukuncin kisan.
Har ila yau, a ranar Talatar da ta gabata ne kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta soki kasar ta a kan abin da ta kira “hanyoyin yanke hukuncinta masu cike da kura kurai.” Daga nan ta bukaci a dakatar da yanke hukuncin kisan.
A kasar yawanci ana fille kan mutanen da aka samu da laifin kisan kai da fashi da makami da safarar miyagun kwayoyi da kuma ridda ne a bainar jama’a.