Saudiyya ta zartar wa wanda ya kai wa ’yan sanda hari hukuncin kisa

An zartar wa wani mutum hukuncin kisa a kasar Saudiyya ranar Talata saboda kai wa wani dan sanda hari tare da ba da mafaka ga wanda ake nema

Saudiyya ta zartar wa wanda ya kai wa ’yan sanda hari hukuncin kisa

Tutar Saudiyya

An zartar wa wani mutum hukuncin kisa a kasar Saudiyya ranar Talata saboda kai wa wani ’yan sanda hari.

Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida ta Saudiyya ta ce an yanke wa Anwar bin Jaafar bin Mahdi al-Alawi hukuncin kisa ne bayan samun sa da laifin bude wa wani ofishin ’yan sanda wuta.

Haka kuma an same shi da laifin baar da mafaka ga wani wanda jami’an saro ke nema kan mallakar makami ba bisa ka’ida ba.

Sanarwar da Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida ta Saudiyya ta fitar ta kara da cewa kisa shi ne hukuncin duk wanda aka samu da irin wannan laifi.

(SPA).

Ban zama Shugaban Kasa don na tara kuɗi ba — Tinubu

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda

‘Yan bindiga sun ƙone gidan mai da motoci 4 a Enugu

Kwalara ta kashe fiye da mutum 300 a Sudan