Saudiyya za ta buga sunaye da hotunan masu yi wa mata yankan-baya

Hukumar gyaran tarbiyyar al’umma, wadda aka fi sani da Hai’a a Saudiyya, za ta rika bayyana sunayen wadanda ke yi wa mata yankan-baya, kuma za ta rika nuna hotunansu a kafafen yada labarai, kamar yadda Shugaban Hukumar, Sheikh Abdullateef Al-Asheikh ya bayyana.Al-Asheikh ya ce a halin yanzu hukumar ta kama mutane uku wadanda ke yankan-baya […]

Saudiyya za ta buga sunaye da hotunan masu yi wa mata yankan-baya

Sheikh Abdullateef Al-Asheikh, Shugaban Hukumar Hai’a na SaudiyyaHukumar gyaran tarbiyyar al’umma, wadda aka fi sani da Hai’a a Saudiyya, za ta rika bayyana sunayen wadanda ke yi wa mata yankan-baya, kuma za ta rika nuna hotunansu a kafafen yada labarai, kamar yadda Shugaban Hukumar, Sheikh Abdullateef Al-Asheikh ya bayyana.
Al-Asheikh ya ce a halin yanzu hukumar ta kama mutane uku wadanda ke yankan-baya ga mata, suna karbar kudi a hannunsu. Ya bayyana wannan hukunci ne a wani bikin karrama jami’an Hai’a da suka kama mutanen suna karbar kudi a hannunsu, a birnin Riyadh.
“Za a buga sunaye da hotunan wadanda aka same su da wannan laifi a kafafen yada labarai, nan da ’yan kwanaki masu zuwa,” a cewar Al-Asheikh. Kuma daukacin mutanen da hukumar ta kama tuni suka amsa laifinsu.
Ya ce Haia ta kama daya daga cikin masu laifi a wata unguwa da ke kira Al-Rawdha. Ya yi wa wata mata da ya sani yankan baya, ta yadda ya rika kutsa kai cikin gidanta. A lokuta da dama har buya ta rika yi a rufin gidan tare da ‘’ya’yanta, don ta tsira daga sharrinsa.
Shi kuwa mutum na biyu da hukumar ta kama, matar ce ta aika masa da wasu hotuna, don haka wannan matashi ya rika yi mata barazanar zai tona mataz asiri. Da matar ta kasa jure wa yankan bayan da mutumin ke yi mata, sai kawai ta kai kara Haia. Da hukuma ta yi yunkurin kama shi, sai kawai mutumin ya yi ta harbinsu, amma bai cutar da kowa ba, har ya shiga hannu. Kuma hukumar ta samu tabar hashish da kwayoyi masu sanya maye a jikin mutumin.
Ita kuwa matsa ta uku, a cewar shugaban, wasu ma’aurata ne aka kama, inda matar ke taimaka wa mijinta ya nemi auren mata, bayan ya yin auren sai ya sake su, ta hanyar dabaru daban-daban. Sai kuma ma’auratan suka rika daukar hotunan suna yi musu barazanar tonon silili ko yankan baya. “An dai kama mutumin ne a lokacin da ya bukaci wata mata ta ba shi Riyal dubu bakwai (wato Naira dubu 28),” inji shi.
Al-Asheikh  ya ce a halin yanzu Hukumar ta  Haia  na binciken wasu laifukan yankan baya a unguwannin Al-Murabba da Al-Musanadah, inda aka samu daruruwan laifuka irin wadannan. Sai dai a cewarsa, hukumar za ta sha wahala wajen shawo kan matsalolin saboda rashin isassun kayan aiki. Don a cewarsa, wasu laifuka  da ake bibiya, sun shafi wasu ’yan mata ne da shekarunsu bai wuce 13 ba, kuma suna da shafukan sadarwar na twitter.