Saudiyya za ta gina benen da ya fi kowane tsawo a duniya

A makon gobe ne kasar Saudiyya za ta fara ginin wani bene wanda idan ta kammala ginasa, shi ne zai zama ginin da ya fi kowane tsowo a duniya.Aikin da ake fatan kammalawa a tsawon shekara biyar, tsowonsa zai kai Kilomita 1 (kimanin kafa dubu uku da dari 2 da 80). Hakazalika, ginin zai dara […]

Saudiyya za ta gina benen da ya fi kowane tsawo a duniya
Saudiyya za ta gina benen da ya fi kowane tsawo a duniya

A makon gobe ne kasar Saudiyya za ta fara ginin wani bene wanda idan ta kammala ginasa, shi ne zai zama ginin da ya fi kowane tsowo a duniya.
Aikin da ake fatan kammalawa a tsawon shekara biyar, tsowonsa zai kai Kilomita 1 (kimanin kafa dubu uku da dari 2 da 80). Hakazalika, ginin zai dara benen da ya fi kowane tsawo a halin yanzu wato Burj Khalifa da ke birnin Dubai da kafa dari 5.  
Ginin da aka rada wa sunan Hasumiyar Saudiyya, an kiyasta aikinsa zai ci zunzurutun kudi har Fan miliyan dari 7 da 80 (kwatankwacin Naira biliyan dari 2 da miliyan 2). Kuma za a yi amfani da filin da ya kai fadin murabba’in mita dubu dari 5,  zai kuma kunshi hawa dari 2 wanda za a girke na’uran hawa bene guda 59.
Wannan aikin dai na daya daga cikin ayyukan da kasar take gudanarwa na gina wani sabon gari arewa da birnin Jeddah wanda ya kai fadin murabba’in mita miliyan biyar da mita dubu dari uku.  
Kodayake, mahukuntar kasar sun ce ginin zai kara fito da birnin Jeddah da ma kasar kanta. Sannan kuma zai samar da karin ayyukan yi ga ‘yan kasar.