Saudiyya za ta rage hako danyen mai da ganga 500,000
Kasar Saudiyya ta dauki matakin rage ganga dubu 500 daga yawan danyen mai da take fitarwa daga watan Yuli har zuwa Disamban 2024.
Kasar Saudiyya ta dauki matakin rage ganga dubu 500 daga yawan danyen mai da take fitarwa daga watan Yuli har zuwa Disamban 2024.
Saudiyya ta dauki matakin ne bayan kasahe masu arzikin mai sun amince su rage adadin danyen man da suke fitarwa bisa yarjejeniyar Kungiyar Kasashe Masu Arzikin Mai da Dangoginsu (OPEC+).
A ranar Lahadi, Ma’aikatar Albarkatun Mai ta Saudiyya ta ce ta dauki matakin rage adadin man da take fitarwa da ganga miliyan daya a watan Yuli, wanda zai karu.
Da haka, yawan danyen man da Saudiyya ke fitarwa zai koma ganga miliyan tara, inda a watan Yuli za a yanke ganga miliyan 1.5.
- Muna bukatar a kara mana ninkin albashinmu sau biyu —Likitoci
- Yadda ’yan bindiga suka kashe mutum 62 a Zamfara da Sakkwato
Ma’aikatar ta ce ta dauki matakin ne daidai da yunkurin kasashen OPEC+ domin samar da wadataccen mai a kasuwa.
Kasashen na OPEC+ sun yi ittifakin fitar da danyen mai ganga miliyan 40.46 zuwa 2024.