Sauke hadiman Gwamnan Kano da siyasar da ke ciki

Ana zargin duk da barin zancen da Sakataren Gwamnatin Kano ya yi, gwamnan ba zai iya taba shi ba, sannan akwai yiwuwar ya dawo da hadimansa da ya sallama nan gaba

Sauke hadiman Gwamnan Kano da siyasar da ke ciki

Amakon shekaranjiya ne Gwamnan Jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya sauke Kwamishinan kasa na Jihar Kano Alhaji Adamu Aliyu Kibiya da kuma Mai ba shi Shawara kan Harkokin Matasa Yusuf Imam (Ogan boye) daga mukamansu sakamkaon wasu kalamai da suka furta a kan abin da ya shafi shari’ar zaben Gwamnan Jihar, kalaman da a ciki suka yi barazana ga alkalan da suke gudanar da shari’ar a lokacin.

A shari’ar, tuni kotun ta soke zaben Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jam’iyyar NNPP, ta ba Yusuf Gawuna na Jam’iyyar APC.

Tun farko Jam’iyyar APC ce ta kai kara tana kalubalantar nasarar da Gwamna Abba ya samu a zaben da aka yi a ranar 18 ga Maris da ta gabata.

A wata ranar Alhamis din makon shekaranjiya kafin yanke hukuncin ne gwamnatin da magoya bayananta suka gudanar da addu’a ta musamman don neman nasara a kan shari’ar inda jim kadan da kammala addu’ar aka jiyo wadancan masu rike da mukaman gwamnatin biyu suka yi kalaman da suka jawo rasa kujerunsu.

Katobarar da hadiman gwamna suka yi

A cikin wani faifan murya da Aminiya ta samu an ji tsohon Kwamishina Adamu Aliyu Kibiya na cewa “Duk wani alkali da ake ba shi kudi yake yanke hukunci muna so mu fada masa cewa daga wannan karon mun gaji, zalunci ya kare. Haka kuma muna fada masa cewa ya zaba tsakanin rayuwarsa kudin da ya karba.”

Haka shi ma Mashawarcin Gwamnan, Imam an ji shi yana cewa “Babu wani dan bakauyiya ko bai iya sa hula ba ka fito daga wani kauyen, saboda kana so ka yi takara 2027.

“Kana so maigidanka ya mutu ka zama Shugaban kasa. Ka ce za ka zo ka birkita mana Kano, To wallahi ba a haifi mutum ba sai dai wallahi idan karar da dukkanmu ’yan Kwankwasiyya za ku yi, amma mun ci zabe babu dan da ya isa ya ce zai kwace mana zabenmu.”

Bayan fitar wadannan kalamai ne kungiyoyim al’umma musamman kungiyar lauyoyi ta kasa reshen Jihar Kano a karkashin jagorancin shugabanta, Barista Sagir Sulaiman Gezawa, ta nuna rashin jin dadi a kan kalaman inda ta nemi Gwamnatin Jihar Kano ta dauki mataki.

Hakan ya sa a cikin daren wannan ranar ta Alhamis Kwamishinan Watsa Labarai na Jihar, Baba Halilu dantiye ya kira taron manema labarai inda ya barranta gwamnatin daga wadancan kalamai da hadiman gwamnati suka yi, kuma ya sanar da cewa gwamnatin ta sauke su daga mukamansu.

Wannan mataki da gwamanti ta dauka ya faranta ran mutane da dama a jihar inda kuma aka yaba wa Gwamnan Jihar Alhaji Abba Kabir Yusuf bisa tauna tsakuwa da ya yi wanda kuma ake ganin zai zama izina ga masu sakin baki a jihar.

Sakataren Gwamnati ma ya yi

Sai dai mutane na ganin cewa akwai sauran rina a kaba, domin a cewarsu kamata ya yi Gwamnan ya cire Sakataren Gwamnatin Jihar Dokta Baffa Bichi daga kan kujerarsa saboda a cewarsu shi ma ya yi irin wannan barin zance inda aka ji yana cewa, “Wasu azzaluman mutane suna can suna kulle-kulle a Abuja don su tayar mana da tarzoma a Kano.

“To muna fada musu cewa a wanann karon ba za mu taba yarda a kwace mana zabe ba. Duk kuma wanda ya taba mana zabe to za a ga ba daidai ba.”

Duk kokarin Aminiya don jin ta bakin gwamnatin game da dalilin da ya hana ta sauke Sakataren Gwamnnati abin ya ci tura.

‘Abba ba zai iya taba Baffa ba’

Sai dai wani na kusa da gwamnatin da ya nemi a boye sunansa ya shaida wa Aminiya cewa Sakataren Gwamnatin yana da karfin da ba za a iya daukar irin wancan makamancin mataki a kansa ba, duba da yadda ya tsaya wa gwamnatin har ta kafu inda ya yi da jikinsa da aljihunsa ana ganin abu ne mai wahala Gwamnan ya iya daga masa kara.

Ba yau farau ba

A daidai lokacin da Gwamnatin Kano ke samun yabo daga al’umma bisa wannan mataki da ta dauka, wasu kuma daga cikin al’ummar gari suna ganin cewa wannan ba wani abin a-zo-a-gani ba ne inda suka yi hasashen cewa nan gaba kadan gwamnatin tana iya bai wa wadanan mutane wasu mukaman, domin hakan ta sha faruwa a jihar, inda gwamnatocin baya suka sauke hadimansu daga baya kuma suka ci gaba da zama tare,

Idan za a iya tunawa a lokacin mulkin Gwamna Ibrahim Shekarau ya sauke mai magana da yawunsa Dokta Sule Ya’u Sule daga mukaminsa a lokacin da ya sanar da duniya game da wata takarda da aka ce wai Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin kasa (EFCC), ta wanke shi inda kuma daga baya aka gano takardar ta jabu ce.

Bayan kura ta lafa gwamnatin ta mayar da Dokta Sule Yai Sule kan kujerarsa wanda kuma har zuwa yanzu wannan alaka ta ci gaba domin har yanzu shi ne mai magana da yawun tsohon gwamnan.

Haka irin hakan ta faru a lokacin gwamnatin Dokta Abdullahi Umar Ganduje inda ya sauke Kwamishinan Ayyuka Injiniya Mu’azu Magaji dan Sarauniya a kan ya yi murnar rasuwar tsohon Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnatin Taraayya Alhaji Abba Kyari wanda ya rasu sakamakon kamuwa da cutar Kwarona.

Sai dai bayan wani lokaci, Ganduje ya sake ba wa dan Sarauniyar wani mukamin inda ya nada shi a matsayin mai ba shi shawara kan sha’anin Kwamitin Gas na AKK Plant tare da daga darajarsa a cikin Majalisar Zartarwa, sai dai daga baya Gwamna Ganduje ya sake cire shi skamakon sukar shugaban kasa Muhamamdu Buhari da ya rika yi.

Har ila yau, makamancin haka ta faru a tsakanin Gwamna Abdullahi Ganduje da Salihu Tanko Yakasai inda ya cire shi daga mukaminsa na Darakta Janar na ’Yan jarida a Gidan Gwamnati sakamakon sukar gwamnatin Shugaba Buhari da ya rika yi, sai dai daga baya ya mayar da shi kan kujerarsa.

Duk da cewa daga baya ya sake cire shi daga kan kujerarsa sakamakon ci gaba da sukar Gwamnatin Buhari da ya yi, sai dai za a iya cewa har yanzu suna tare duk da cewa dawisun ya koma Jam’iyyar PRP har ya yi mata takarar Gwamna.

Domin a kwanan nan an gan shi ya je Abuja wajen Shugaban Jam’iyyar APC na kasa wanda kuma uban gidansa ne na siyasa wato Dokta Ganduje inda ya koma jam’iyyar ta APC.

Abin jira a gani shi ne yadda za ta kaya ko alaka za ta ci gaba a tsakanin Gwamna Abba Kabir Yusuf da wadanda Gwamnan ya sauke daga mukamansu ko akasin hakan.

Tinubu ya yi naɗin sabbin muƙamai huɗu

Majalisar Zartarwa ta amince da kusan Naira tiriliyan 50 Kasafin Kuɗin 2025

Tinubu ya jagoranci zaman Majalisar Zartarwa

HOTUNA: Ana shirye-shiryen jana’izar marigayi Lagbaja