Saura kiris Jose Mourinho ya yi wa alkalin wasa duka
Sai da aka yi da gaske kafin hana shi afka wa alkalin wasa.
Saura kiris mai horas da ’yan wasan kungiyar kwallon kafa ta AS Roma, Jose Mourinho ya lakada wa alkalin wasa duk yayin wasann mako na bakwai na gasar Serie A da kungiyar ta fafata a ranar Lahadi.
Sai da jami’an da ke taimakawa Jose Mourinho suka yi da gaske kafin hana shi afka wa alkalin wasa da duka.
- El-Rufai ya so a kai Film Village Kaduna, amma… —Sani Mu’azu
- Kotu ta yanke wa Evans hukuncin shekaru 52 a gidan wakafi
A daidai minti na 57 ne alkalin Daniele Chiffi ya kore shi daga fili a wasan da AS Roma ta sha kashi a hannun Atalanta da ci 1-0 a gaban ’yan kallo dubu 60.
Mourinho mai shekaru 59 ya shiga filin wasa ne domin fuskantar alkalin wasa saboda hana su damar bugun fanaretin da yake ganin kungiyarsa ta cancanci a ba ta.
Lamarin ya samo asali ne bayan da ake zargin Caleb Okoli na Atlanta da yi wa Nicolo Zaniolo keta a cikin da’irar yadi na 18 a minti na 54 da fara wasa.
Sai dai a maimakon bai wa Roma damar bugun daga kai sai mai tsaron raga, sai alkalin wasan ya bai wa Atlanta damar bugun tazara.
Bayan korar Mourinho daga fili dai magoya bayan AS Roma sun rika rera wakar goyon bayan kocin nasu domin kara masa kwarin gwiwa.
Wannan dai ba shi ne karo na farko da alkalin wasa yake bai wa Jose Mourinho jan kati tare da korarsa daga filin wasa ba.
Akwai lokuta da dama da kocin kai mayar da ire-iren wannan zafafan martanin a duk lokacin da bai gamsu da matakan da aka dauka kan ’yan wasa ko kungiyar da yake horaswa ba.