Saura kiris na yi gudun hijira, Inji Buhari
Shugaba Muhammadu Buhari ya ce saura kiris ya yi gudun hijira zuwa wata kasa inda a ce ba a samu damina mai kyau ba a tsawon shekaru biyu da suka gabata. Buhari ya yi furucin ne yayin da ya karbi tawagar kungiyar sakarakunan gargajiya wanda Sarkin Musulmi Sultan Muhammad Sa’ada Abubakar a fadarsa da ke […]

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce saura kiris ya yi gudun hijira zuwa wata kasa inda a ce ba a samu damina mai kyau ba a tsawon shekaru biyu da suka gabata.
Buhari ya yi furucin ne yayin da ya karbi tawagar kungiyar sakarakunan gargajiya wanda Sarkin Musulmi Sultan Muhammad Sa’ada Abubakar a fadarsa da ke Abuja, a jiya.
“Mun yi sa’a a shekarar da ta gabata da kuma shekarar da muke ciki an sami damina mai kyau. Idan da ba ta yi kyau ba da yanzu ina tunanin wace kasa zan yi gudun hijira amma sai Allah ya amsa addu’ar ’yan Najeriya. Damina ta yi kyau shekarar da ta gabata da kuma wannan shekara. Rahotannin da nake samu sun nuna cewa ta yi kyau. Mun gode wa Allah idan da an samu akasin haka da mun sami matsaloli masu yawa”. Inji shi