Saura minti 30 su fashe

Wani direba ne a Legas, ’yan sanda suka tsare shi suka ce ya yi laifi, don haka sai ya ba su Naira dubu hamsin ko su kai shi Alausa. Ya hada su da Allah su kyale shi suka ce: “Ai mu ba aikin Allah muke yi ba.” Nan da nan sai ya kama dariya, ya […]

Saura minti 30 su fashe
Saura minti 30 su fashe

Wani direba ne a Legas, ’yan sanda suka tsare shi suka ce ya yi laifi, don haka sai ya ba su Naira dubu hamsin ko su kai shi Alausa. Ya hada su da Allah su kyale shi suka ce: “Ai mu ba aikin Allah muke yi ba.” Nan da nan sai ya kama dariya, ya dauko wayarsa ya fara magana, yana cewa: “Ranka ya dade, saura minti 30 su fashe, amma bama-bamai 20 ne kawai na dauko, sun ce za su kai motar Alausa, ina nan dawowa da rai yanzu.” Kafin ka ce kwabo, ’yan sandan nan duk sun tsere. Direba ya gama wayarsa ta karya ya wuce da motarsa.
Daga U. S. A. Babawo Yola, 08035038759.

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya