Saurayi da budurwa
Wani Bakatsine ne ya je hira wajen budurwarsa, bayan sun gama zai tafi sai ya sa hannu a aljihu ya dauko kudi ya mika mata. Sai budurwar ta ce ba za ta karba ba. Shi kuma ya ce: “To tun da ba ki so, ni ma ba na so.” Sai ya yi watsi da kudin […]
Wani Bakatsine ne ya je hira wajen budurwarsa, bayan sun gama zai tafi sai ya sa hannu a aljihu ya dauko kudi ya mika mata. Sai budurwar ta ce ba za ta karba ba. Shi kuma ya ce: “To tun da ba ki so, ni ma ba na so.” Sai ya yi watsi da kudin a nan, kowa ya kama gabansa. To ashe ita wannan budurwa ba tafiya ta yi ba, ta dan labe ne a wani waje a gidan, da niyyar idan saurayin ya tafi ta zo ta kwashe kudin. Haka shi ma Bakatsine bai tafi ba, ya dan labe a kofar gidan da niyyar idan yarinyar ta shiga gidan ya zo ya kwashe kudinsa.
To dama a cikin soro suke zancen kuma an dauke wuta, can sai saurayin da budurwar suka dawo cikin soron, suka fara laluben kudin ba tare da kowannensu ya ga dan uwansa ba. Can sai aka kawo wuta, nan take sai Bakatsine ya wayance ya ce wa budurwar: “Don Allah ba ki ga wayata ba?” Ita ma budurwar ta ce masa: “Ni ma don Allah ba ka ga sarkata ba?”
Daga Isah Ramin Hudu Hadeja 08060353382.