Saurayi da budurwa (2)

Wani saurayi ne ya je wajen budurwarsa suna tattaunawa kuma ga yadda hirarsu ta kasance: Saurayi: Ladidi an tashi lafiya?Budurwa: Ta yi shiru, ta ki amsawa.Saurayi: Ladidi, an kusa daura mana aure amma har yanzu ba ki daina yi mini wulakanci ba.Babudurwa: Hummn, can maka dai!Saurayi: Dama ba wani abu ne ya kawo ni ba […]

Saurayi da budurwa (2)
Saurayi da budurwa (2)

Wani saurayi ne ya je wajen budurwarsa suna tattaunawa kuma ga yadda hirarsu ta kasance:

Saurayi: Ladidi an tashi lafiya?
Budurwa: Ta yi shiru, ta ki amsawa.
Saurayi: Ladidi, an kusa daura mana aure amma har yanzu ba ki daina yi mini wulakanci ba.
Babudurwa: Hummn, can maka dai!
Saurayi: Dama ba wani abu ne ya kawo ni ba illa in tambaye ki ko kin iya tuki. Domin ina son matata ta kware a tuki.
Budurwa: Hmmmn, Tanimu ke nan. Shi ya sa nake matukar son ka.
Saurayi: Hummm!
Budurwa: To wace irin mota za ka saya mini?
Saurayi: Mota kuma?
Budurwa: Eh mana, ba yanzu ka tambaye ni ko na iya tuki ba.
Saurayi: Tafdijam! Ni fa tukin tuwo nake nufi, domin kuwa buhun masara aka ba ni kyauta.
Daga Abubakar Malami