Saurayi da budurwa sun yi bikin baikonsu a gidan zaki
Wani mai wasa da namun daji dan kasar Masar, Mohammad Al Yamani ya shigar da budurwarsa cikin kejin zaki, inda ya rataya mata mesa don murnar bikin baikon da aka yi musu, kamar yadda jaridar Al Masry Al Youm ta ruwaito. A kowane gefen wadannan saurayi da budurwa akwai zaki tsaye. Mintuna kadan da fara […]
Wani mai wasa da namun daji dan kasar Masar, Mohammad Al Yamani ya shigar da budurwarsa cikin kejin zaki, inda ya rataya mata mesa don murnar bikin baikon da aka yi musu, kamar yadda jaridar Al Masry Al Youm ta ruwaito.
A kowane gefen wadannan saurayi da budurwa akwai zaki tsaye. Mintuna kadan da fara da wannan wasa a birnin tashar jiragen ruwa ta Suez Canal, sai aka bayyana wa ’yan kallo cewa, ‘saurayi da budurwsa ne ke bikin murnar baikonsu da aka yi.
Al Yamani mai shekara 23 ya bai wa amaryarsa kyautar zinari, su kuwa ’yan kallo sai tafi suke yi musu, kamar yaddda kafafen yada labaran Masar suka ruwaito.
’Yan uwa da abokan ma’auratan sun rika tsuma a lokacin da suke kallon was an. Shi kuwa Al Yamani dan gado ne, domin mahaifinsa ma tsohon mai wasa da namun daji ne, don hakla ya ce burinsa ya yi bikin baiko irinsa na farko a duniya da ya gudana a kejin zaki.
“Duk da kwarin gwiwar amaryata, na ga alamun tsoro a fuskarta a lokacin da muka shiga kejin zakio,” inji shi. “Na jajirce wajen ba ta kariya daga kowane hadari. Don haka da na fahimci wani zaki bai gamsu da ganinta (amaryata ba) , kuma ya ki yarda ya bi umarnina , sai na bayar da umarnin a cire mini shi daga kejin,” inji shi.