Saurayi ya kai kansa lahira

Wani saurayi dan Shekara 32 mai suna Malam Rabi’u Muhammad da ke kauyen dantsinke a karamar hukumar Kumbotso ta jahar Kano ya yi ajalin kansa da kansa bayan da ya yanke makogwaronsa da Al’aurarsa a yunkurinsa na kashe kansa.Muhammad bai mutu ba a lokacin da ya aikata wannan danyen aikin sai bayan da aka kai […]

Saurayi ya kai kansa lahira
Saurayi ya kai kansa lahira

Wani saurayi dan Shekara 32 mai suna Malam Rabi’u Muhammad da ke kauyen dantsinke a karamar hukumar Kumbotso ta jahar Kano ya yi ajalin kansa da kansa bayan da ya yanke makogwaronsa da Al’aurarsa a yunkurinsa na kashe kansa.
Muhammad bai mutu ba a lokacin da ya aikata wannan danyen aikin sai bayan da aka kai shi Asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano don ceto ransa.
Wata majiya mai tushe ta tabbatar wa Aminiya cewa, Marigayi Muhamadu ya rasu bayan da likitoci suka yi masa aiki a al’aurarsa da kuma makogwaronsa domin ceto ransa amma hakan ba ta samu ba.
Kakakin Rundunar ‘Yan sanda na Jahar Kano, ASP Musa Magaji Majiya wanda ya tabbatar da afkuwar al’amarin, ya shaida wa Aminiya cewa saurayin ya yi ban kwana da duniya ne bayan kwanaki biyu da afkuwar al’amarin.
Wani abokin marigayin ne mai suna Burhanaddeen Abdullahi ya fara gano halin da Muhammad yake ciki a lokacin ya kai masa ziyara gidansa.
Abdullahi ya bayyana cewa, ya je wajen Muhammad domin su gana amma sai ya tarar da kofar dakinsa a rufe, al’amarin da bai saba gani ba a duk lokacin da ya kai masa ziyara.
“Na yi matukar mamaki a lokacin da na ga kofar dakinsa a rufe. Don haka sai na buga kofar domin a bude amma babu wanda ya amsa min. Bayan da na buga sosai amma ban ji motsin kowa ba sai na shaida wa mutanen da ke nan kusa wadanda suka taimaka min wajen ci gaba da buga kofar, amma duk a banza babu motsin kowa,” inji Abdullahi .
Abdullahi ya kara da cewa, “bayan bugun kofar na lokaci mai tsawo sai aka yanke shawarar an balle kofar, kuma ko da ballewa sai muka tarar da Muhammadu cikin jini male-male kuma ga al’aurarsa a gefe sannan makogwaronsa ma na zubar da jini sakamakon kokarin yanke shi da aka yi. Ganin haka sai na garzaya  ofishin ‘yan sanda da ke Na’ibawa na shaida musu abin da ya faru, inda a sakamakon haka aka garzaya da shi asibiti don ceto ransa.’’
Ya ci gaba da cewa, ‘’da farko mun je Abisitin Murtala ne amma aka tura mu Asiibitin Nasarawa, daga nan kuma aka tura mu Asibitin Koyarwa na Malam Amini Kano.’’
“Ba bu wanda zai ce ga dalilin da ya sa Muhammad ya aikata wanna danyen aiki a yanzu, domin a lokacin da al’amarin ya faru babu kowa a gidan sai shi kadai, domin  yayansa da iyalinsa sun yi tafiya,” in ji Abdullahi.
Malam Ahmad yana daga cikin makwabtan gidan da Malam Rabi’u ke zaune, ya shaida wa Aminiya cewa, a lokacin da suka ji shiru ba su ga Malam Rabi’u ya fito daga gidan ba sai suka yi shawarar balle kofar gidan inda suka iske shi kwance cikin jini male-male da shaidar yanka a makogoransa, sannan a gefe guda kuma ga wuka a ajiye,wacce aka yi amfani da ita wajen yanke al’aurarsa. “Wannan gida da yake zaune a ciki gidan dan uwansa ne, wanda yake kula masa da shi, kasancewar shi ba ya garin. Lokacin da ba mu ga gilmawarsa ba kamar yadda ya saba, sai muka yanke shawarar shiga gidan mu duba, inda muka ga dakin da yake ciki a kulle, nan muka balle kofar dakin inda muka shiga muka same shi kwance cikin jini ga shaidar yanka a wuyansa. Sannan ga al’aurarsa an yanke an kuma ajiye a gefe guda.” Inji shi
Binciken da Aminiya ta gudanar  ta gano cewa marigayi Malam Rabiu ba shi da wani tarihi na tabuwar hankali, haka kuma ba a samu labarin faruwar wani sabani tsakaninsa da wani mutum a Unguwar ba.
Wani da ya nemi a boye sunansa, ya bayyana shakkunsa game da faruwar lamarin, inda ya dora alhakin faruwar lamarin akan wadansu bata-gari, domin a cewarsa, babu yadda za a yi mutum ya yi wa kansa wanann danyen aiki.