Saurayi ya kashe dan basarake a kan buduruwa
Wani saurayi mai kimanin shekara 18 da ke zaune a Unguwar Karofin Madaki a garin Bauchi ya shiga hannun ’yan sanda bisa zargin aikata kisa. Ana zargin matashin ya kashe wani mai suna Hamza Usman mai shekara 23 da ke Unguwar Mahaukata a cikin garin Bauchi ne a kan budurwa. ASUU da Gwamnati sun sasanta […]
Wani saurayi mai kimanin shekara 18 da ke zaune a Unguwar Karofin Madaki a garin Bauchi ya shiga hannun ’yan sanda bisa zargin aikata kisa.
Ana zargin matashin ya kashe wani mai suna Hamza Usman mai shekara 23 da ke Unguwar Mahaukata a cikin garin Bauchi ne a kan budurwa.
- ASUU da Gwamnati sun sasanta
- Ya tsere ya bar matarsa a asibiti bayan ta haifi ’yan uku
- Ann kubutar da matashi bayan awa bakwai a cikin kwata
A zantawar da ya yi da Aminiya a ofishin ’yan sanda na cikin garin Bauchi, wanda ake zargin ya ce ya samu labari ne cewa Hamza ya zo neman sa da rana a unguwarsu a kan zai yi masa rauni kuma ya zo da adda a kugunsa, yana gyara ta shi kuma sai ya gudu ya bi shi da gudu bai same shi ba.
Ya ce lallai babu wani abin da ya hada su da marigayin sai dai yana son wata budurwa ce shi ma yana son ta.
Ya ce da mamacin ya biyo shi bai same shi ba, shi ma Kabirun sai ya bi shi gidansu da dare ba ya nan.
Daga nan ne sai ya bi shi gidan su budurwar yana so ya yi mata magana, sai ya cire wuka a jikinsa.
Ya ce ya gaya masa ba zai iya yin fada da shi a nan ba sai
dai su hadu a wani wuri.
Kabiru ya ce da marigayin ya biyo shi sai ya fadi a kusa da masallaci, shi kuma ya soka masa wuka ba da niyyar ya kashe shi ba, sai Allah Ya kaddari kwanansa ya kare ya rasu.
Ya ce bayan ya daba wa marigayin wukar ya cire wukar ya jefar da ita a hanya, inda ya kara da cewa ya ga marigayin yana
yawan bin sa yana nemansa da fada ne ya sa ya dauki wannan mataki.
Wanda ake zargin ya ce ya yi nadamar abin da ya aikata saboda lokacin da Hamza ya bi shi da adda da ya kai kararsa wajen hukuma
da hakan ba za ta faru ba, amma sai bai yi ba, sannan ya ce yana rokon iyayensa da iyayen Hamza su gafarce shi.
Ya shawarci matasa ’yan uwansa su guji biye wa zuciya, kuma idan wani ya nemi yi musu ta’addanci don guje wa aikin da mutum zai yi nadama su guji ramawa da makami, maimakon haka su kai kararsu wajen hukuma domin a bi kadinsu ko a sasanta.
Hukuma ta bi mana kadi
—Mahaifin marigayin
Alhaji Lawal Ahmed Aliyu, wanda shi ne ke rike da sarautar Mahaukatan Bauchi, ya ce Hamza dansa ne, kuma yana sana’ar gyaran janareta ne.
Ya ce ba abin da za su ce sun bar komai ga Allah da kuma hukuma ta bi musu kadin wannan zalunci da aka yi musu.
Alhaji Lawal ya ce budurwar da ake magana a kanta sun zauna da iyayenta da su kuma an ba Hamza ita sun yi musu baiko, har mahaifinta ya ce tunda an ba Hamza ita, to yanzu in ya je hira ya rika shiga suna hira a cikin gida.
“A makon da ya wuce ne ma muka zanta da mahaifinta a kan za a sanya ranar auren yaran”, inji shi.
Ya ce har cikin gidan da suke hirar aka bi Hamza aka kashe shi kuma daga bisani ’yan sanda suka kama wanda ya yi kisan yanzu suna saurare ne su ji me hukuma za ta yi a kansu.
Ya bayyana mamacin da yaron kirki, mai hankali da ladabi da biyayya da kwazon neman abin kansa.
Kuma ya ce bai taba jawo musu wata fitina a gida ba, kullum idan ya je wajen sana’arsa ya dawo sai ya je ya gaida mahaifiyarsa daga bisani ya tafi wajen budurwar da zai aura.
Mun kama wanda ake zargi—’Yan sanda
Tun farko, Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Bauchi, DSP Mohammed Ahmed Wakil ya ce wanda ake zargin ya je wajen Hamza ne ya same shi a wajen budurwarsa ya soke shi da wuka a kirji, nan take jini ya yi ta zuba, aka dauke shi zuwa asibiti inda likita ya ce ya rasu.
Wakil ya ce da ’yan sanda suka samu labari sai suka je neman wanda ake tuhuma suka kuma samu nasarar kamo shi.
Ya ce a lokacin da suke bincike wanda ake zargin ya ambaci sunayen wadansu mutum biyu da ya ce suna da hannu a ciki, wadanda dukkansu biyun sun gudu,
’yan sanda na nemansu ruwa a jallo.
Wakil ya ce Kwamishinan ’Yan sandan Jihar, Lawal Tanko Jimeta ya ba da umarnin duk inda aka gan su a kamo su kuma a mai da binciken lamarin Sashen Binciken Manyan Laifuffuka na Rundunar domin yin bincike mai zurfi.
Ya ce da zarar an kammala bincike za a gurfanar da wadanda ake zargi a gaban kotu domin a yi musu hukunci.
Kwamishinan ya nanata kudirin rundunar na yin amfani da dukkan kayayyakin aikin da ke ikonta domin tabbatar da kare rayuka da dukiyoyin jama’a a jihar.
Sannan ya roki jama’a su rika bai wa ’yan sanda labarin masu aikata miyagun
laifuffuka.