Saurayi ya kawata wurin zaman fasinjojin jirgin kasa don budurwarsa
Fasinjoji sun cika da mamaki a kasar Sin, a wani gari da ake kira di’an, lokacin da wani suarayi ya kawata mazaunin mata a jirgin kasa, ranar 24 ga Oktobar bana. daukacin wuraren zaman fasinjojin duk ya kawata su da fastoci, wadamnda ke dauke da sakonni Tingting ki aure ni! Wang Yin, wannan saurayi ya […]
Fasinjoji sun cika da mamaki a kasar Sin, a wani gari da ake kira di’an, lokacin da wani suarayi ya kawata mazaunin mata a jirgin kasa, ranar 24 ga Oktobar bana. daukacin wuraren zaman fasinjojin duk ya kawata su da fastoci, wadamnda ke dauke da sakonni Tingting ki aure ni! Wang Yin, wannan saurayi ya zauna akan gwiwoyinsa rike da furanni 108 da kuma zobe a daya hannunsa, inda yake kiran budurwarsa:
“Tingting, haduwa da ke ita ce babbar sa’ar rayuwata. Don Allah amaryata, ki zamanto tauraruwar sa’ata ta har abada.”
Wang ya ce a lokacin da suka fara soyayya babu irin wannan abin daukar fasinjoji na zamani a birnin. Sabod ahaka suka yi wa juna barkwanci cewa za su kawata wannan wurin zaman fasinjojhi da ke jirgin kasa. daukadin wadancan shekaru da suka gabata, sai kawai Wang ya yanke shawarar bijiro wa kansa da tambaya. Saboda ya shammaci budurwarsa, ya kawata daukacin wurin daukar fasinjojin da ke cikin jirgin kasa don cika mata a lkawarinsa.