Saurayi ya rataye kansa saboda damuwa

Wani matashi mai kimanin shekara 27 da ke zaune a Unguwar Shekar Maidaki a Karamar Hukumar Kumbotso a Jihar Kano, ya rataye kansa. Matashin mai suna Nasiru Ali Abdussalam, an same shi ne a mace ranar Juma’ar da ta gabata da misalin karfe tara na safe, yayin da wadansu abokan kasuwancinsa suka zo karbar bulo […]

Saurayi ya rataye kansa saboda damuwa

Marigayi Nasiru a hagu tare da abokinsa Hassan

Wani matashi mai kimanin shekara 27 da ke zaune a Unguwar Shekar Maidaki a Karamar Hukumar Kumbotso a Jihar Kano, ya rataye kansa.

Matashin mai suna Nasiru Ali Abdussalam, an same shi ne a mace ranar Juma’ar da ta gabata da misalin karfe tara na safe, yayin da wadansu abokan kasuwancinsa suka zo karbar bulo da suka saya a wajensa, inda aka tarar ya rataye kansa a jikin raftar dakinsa.

Akwai rahontanni da suke cewa mamacin ya rataye kansa ne sakamakon bacin rai da ya shiga dalilin neman aure da ya sha yi na tsawon wasu shekaru amma mahaifiyarsa tana hana shi.

A tattaunawarta da Aminiya, mahaifiyar mamacin, mai suna Malama Amina Umar Ahmad, ta ce ’yan kwanaki kadan kafin rasuwarsa, yakan fadi wasu maganganu kamar cewa wanda ya mutu yanzu ya huta da wahalhalun rayuwar da ake fama da su.

Malama Amina ta ce kimanin shekara shida da suka wuce Asibitin Malam Aminu Kano ya gano cewa mamacin yana fama da cutar damuwa inda suka dora shi a kan magani.

“Tun daga wancan lokacin yake shan maganin, koda yake wani lokaci sai na tilasta masa yake sha. Mutum ne natsatstse amma duk lokacin da ciwon ya dawo masa za ka fahimci cewa yana cikin damuwa amma sai kana kusa da shi,” inji mahaifiyar.

Ta ce an kai lokacin da Nasiru ba ya yarda ya sha maganin har sai ta daka ta zuba masa cikin abincinsa. Daga karshe ta ce sai da ta koma asibitin suka canja kwayoyi da allurar da ake masa batan-dabo da cewa maganin gyambon ciki ne.

Malama Amina ta  ce damuwar marigayi Nasiru ta samo asali ne kimanin shekara 13 da suka gabata lokacin da suka rabu da mijinta, wanda hakan ya sa ta kwashe ’ya’yanta suka bar gidan.

Ta yi zargin cewa mahaifin Nasiru ya kore shi yayin da shi marigayin ya zabi ya zauna tare da ita.

“A lokacin da muka zo nan babu komai bayan gonaki, mu kadai muka zauna a nan, daga baya mutane suka taru. Amma lokacin da na auri mijina na yanzu sai kishi ya kama tsohon mijina ya ce sai na ba shi ’ya’yansa, ni kuma na ki, sakamakon haka muka je gaban alkali.”

Game da batun yanayin mutuwarsa kuwa, “Akwai rade-radi da ake cewa wai na hana shi aure kuma haka ne dalilin mutuwarsa. Wannan rashin adalci ne a fadi haka. Mutane suna fadin haka ba tare da la’akari da irin wahalar da na sha wajen rainonsu ba. Muna kan tattaunawa da kannensa mu ga yadda za a bullo wa maganar aurensa wannan abu ya zo ya auku. Amma kamar yadda ka sani aure ba ya yiyuwa ba a shirya sosai ba.”

Daya daga cikin makwabta kuma abokin marigayi Nasiru, mai suna Hassan Sulaiman Adam, ya bayyana wa Aminiya cewa suna tare da marigayin kimanin shekara bakwai, inda ya ce ya lura akwai abin da yake damun Nasiru amma ya ki ya bayyana wa kowa saboda abu ne da ya shafi iyayensa.

Hassan ya ce ba adalci ba ne a jingina alhakin rasuwar Nasiru a kan mahaifiyarsa, kamar yadda ake yadawa.

Da yawa daga cikin masu jaje da suka zanta da aminiya sun bayyana kaduwarsu game da rasuwar marigayi Nasiru, inda suka bayyana shi da natsattsen mutum wanda ba za a taba kawo masa aikata irin  wannan danyen aiki ba.

A yayin da aka tuntubi, Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano, ASP Abdullahi Haruna, ya tabbatar da aukuwar lamarin inda ya ce Kwamishinan ’Yan sandan jihar ya bada umarnin a yi cikakken bincike don gano musabbabin rasuwarsa.