Saurayin da ya yi lalata da akuya ya ce ya nemi izininta
An kama wani saurayi dan kasar Malawi mai suna Kennedy Kambani mai shekara 21 yana lalata da akuya, inda ya ce sai da ya nemi izinin akuyar kafin ya yi lalata da ita. Mai akuyar ya ce, ya yi zaton Kennedy Kambani zai sace akuyar ce, sai ya gaya wa makwabta su rika kula da […]
An kama wani saurayi dan kasar Malawi mai suna Kennedy Kambani mai shekara 21 yana lalata da akuya, inda ya ce sai da ya nemi izinin akuyar kafin ya yi lalata da ita.
Mai akuyar ya ce, ya yi zaton Kennedy Kambani zai sace akuyar ce, sai ya gaya wa makwabta su rika kula da shi. Ya ce bayan ya dawo gida ne makwabtansa suka ce sun kama Kennedy Kambani yana yi wa akuyar fyade.
Sufeto Lubrino Kaitano ya ce, “Mai akuyar, Mista Pemphero Mwakhulika ya yi tunanin Kambani zai saci akuyar ce, sai shi kuwa ya sanar da jama’a abin da ke faruwa.”
Bayan da jama’a suka halarci harabar da aka kama Kambani, sai suka razana ta yadda suka kama shi yana yi wa akuyar fyade.
Bayan kama Kambani an mika shi ga ofishin ’yan sanda don laifin yi wa dabba fyade. Sai dai a bangarensa, bai amsa laifin fyade ba, saboda ya ce sai da ya nemi izinin akuyar kafin ya fara lalata da ita.
Akuyar tana daya daga cikin wadanda suke kiwo a wajen kauyen Mchinji da ke kasar Malawi.
Wani rahoto ya ce, a watan Nuwamban bara an kama wani mai suna Reuben Mwaba mai shekara 22 yana yi wa akuyarsa fyade a garin Kasama na kasar Zambiya.
Kuma a watan na Nuwamba an kama wani mai suna Feselani Mcube mai shekara 33 yana yi wa akuyar makwabcinsa fyade a gadonsa da ke unguwar Winterbeldt, a kasar Afirka ta Kudu.