Saurayin Mai Awara Ya Watsa Mata Tafasasshen Mai A Zariya

Ya yi mata wanka da tafasasshen mai ne saboda ta yi masa magana bayan ya yi ta daukar awaran da take suya yana ta ci

Saurayin Mai Awara Ya Watsa Mata Tafasasshen Mai A Zariya

Saurayin wata budurwa mai sana’ar awara ya yi mata wanka da tafasasshen mai da take suya da shi a yankin Samarun Zariya da ke Jihar Kaduna.

Matashin ya yi wa buduwar tasa mai suna Hussaina wannen danyen aiki ne saboda ta nemi taka masa burki a wurin sana’arta, yayin da lokacin yake tsaka daukar awarab da take soyawa yana cin.

Bayan saurayin ya yi ta daukar awara yana a dangwalala a yaji yana ci ne Hussaina ta ya masa magana cewa ya daina, lamarin da ya kai ga cacar baki a tsakanin masoyan.

Amma jama’a da ke wurin suka shiga tsakani aka raba su, shi kuma gogan ya yi tafiyarsa.

Ashe labewa ya yi ba wuce ba, daga bisani kafin su ankara ya zo ya dauki kaskon suyan awarar ya antaya mata tafasasshen man a jikinta.

A halin yanzu dai, iyayen Hisssana, wadanda masu karamin karfi ne da suka dogara da sana’ar, suna rokon jama’a da kungiyoyin kare hakkin dan Adam su kawo musu dauki domin yi mata magani da kuma kwato mata hakki.

Shaidu sun bayyana cewa saurayin da ake zargi ya yi wa budurwar wannan aika-aika ya yi kaurin suna wajen tayar da zaune tsaye.

Wani shaida ya bayyana cewa a kwanakin baya wanda ake zargi ya caka wa wani matsahi almakashi, lamarin da ya yi sanadin mutuwar barin jikinsa.