Sauro ya sa wani asarar gilashin mota na fiye da Naira dubu 424
Lange-lange mai ramar keta. Ramamme firgita kato… wannan wani bangare ne na kirarin da Bahaushe ke yi wa sauro. Kuma sai ga shi sauron ya sa wani mazaunin Gabashin China mai suna Lou wanda ya fito daga garin Jiading a Lardin Zhejiang ya fasa gilashin motarsa a kokarinsa na kashe saurona ranar 11 ga Satumban […]
Lange-lange mai ramar keta. Ramamme firgita kato… wannan wani bangare ne na kirarin da Bahaushe ke yi wa sauro. Kuma sai ga shi sauron ya sa wani mazaunin Gabashin China mai suna Lou wanda ya fito daga garin Jiading a Lardin Zhejiang ya fasa gilashin motarsa a kokarinsa na kashe saurona ranar 11 ga Satumban nan
Lou ya yi amfani da hannunsa wajen kokarin kashe sauron da ke gaban gilashin motarsa kirar BMW, inda nan take gilashin ya fashe. Shirin labarai na1818 huangjinyan na gidan talabijin Zhejiang Tb ne ya ruwaito haka a ranar Lahadin da t agabata.
Wani faifan bidiyo ya nuna yadda gilashin ya fashe ya kai gurbin hannu matashi kuma kudin gilashin ya kai kudin China Yuam 8,000 (kimanin Naira dubu 424 da 16 da kwabo 28). Lou ya ce, bai da laifi, illa matsalar daga gilashin ne. Lou ya ajiye motar a gaban kantin gilashin mota na 4S bayan aukuwar lamarin.
Sai dai manajan kantin 4S Huang ya bayyana wa Zhejiang Tb cewa ba su taba samun irin wannan rahoto ba. Lou ya ce, bayan kwana uku da aukuwar lamarin kantin 4S ya canja gilashin kyauta bayan sun binciki motar inji Zhejiang Tb.