Sauyin yanayi: Masana sun shawarci manoma kan lokacin shuka

Wani kwararre a kan aikin gona, Mista Emeka Okoli ya yi kira ga manoma su daidaita lokacin da suke shuka amfaninsu don guje wa fadawa cikin asara. Mista Okoli, wanda shi ne Daraktan Ayiyukan Fasaha, a Ma’aikatar Gona ta Jihar Anambra, ya ba da shawarar ce a wata tattaunawa da ya yi da Kamfanin Dillancin […]

Sauyin yanayi: Masana sun shawarci manoma kan lokacin shuka

Wasu manoma a gona

Wani kwararre a kan aikin gona, Mista Emeka Okoli ya yi kira ga manoma su daidaita lokacin da suke shuka amfaninsu don guje wa fadawa cikin asara.

Mista Okoli, wanda shi ne Daraktan Ayiyukan Fasaha, a Ma’aikatar Gona ta Jihar Anambra, ya ba da shawarar ce a wata tattaunawa da ya yi da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a Awka, babban birnin Jihar Enugu.

Ya ce, an samu canjin yanayin ruwan sama a cikin shekara ukun da suka gabata, sakamakon sauyin yanayi, kuma hakan ya haifar da karancin amfanin gona ga manoman da ba su da kayan ban ruwa a yankunansu.

“Manoman da ba sa aikin ban-uwa ya kamata su kula kada su shuka iri kamar, shinkafa, masara da rogo a cikin kasa mai yashi, amma idan suna da kasa mai yumbu wanda take kunshe da danshi za su iya ci gaba da shuka su.

“Wannan saboda yanayin da muka lura a cikin shekara uku da suka gabata ya nuna cewa, a wasu wurare, ba a samun ruwan sama mai yawa da zai iya ci gaba da fitar da tsirrai.

Don haka, dole manoma su daidaita yanayin shuka don kada su yi asarar amfanin gonakinsu; lokacin da ya dace don shuka, wannan lokacin shi ne daga ruwan sama na farko ya fara a cikin shekara har zuwa mako na biyu na Yuli da farkon watan Satumba; wadanda suke da wuraren ban-ruwa ba su da wata matsala,” inji shi.

Mista Okoli ya ce, amfanin gona yana bukatar isasshen ruwan sama a cikin wata biyu na farkon yin shuka don samun ingantaccen amfani, rashin samun hakan zai iya sa kasar noman ta fitar da amfanin gonar da zai iya mutuwa.

A wani rahoto mai kama da haka, wani manomi mazaunin Abuja, Mohammed Ndana ya shawarci manoma masu sha’awar noman wake su fara shuka tun yanzu.

A tattaunawar da Aminiya t a yi da shi ta tarho, Ndana ya ce, lokacin da ya fi dacewa a shuka waken shi ne daga tsakiyar watan Agusta saboda yanayin ruwan sama a yanzu.

“Kun ga, noman wake, amfanin gona ne mai dadi domin idan kuka shuka shi da wuri kuma ruwan sama ya dade, akwai yiwuwar kila ba zai yi kyau ba, saboda amfanin gona irinsa ba ya son ruwan sama mai karfi yayin da ya fara fitar da fure.

“Haka kuma idan kuka shuka shi a makare ko aka samu daukewar ruwan sama da wuri, amfanin gona ma ba zai yi kyau ba, don haka mafi kyan lokacin shuka wake, shi ne yanzu, kuma manoma musamman wadanda suke yankunan Arewa ya kamata su fara nan take,” kamar yadda ya ba da shawarar ga manoma.