Sayar da rake ya fi aikin gwamnati rufin asiri- Adamu Musa
Alhaji Adamu Musa shi ne Shugaban kungiyar masu sayar da rake a Jihar Bauchi. A cikin tattaunawarsa da wakilinmu a ofishinsa da ke Bauchi a ranar Lahadi, ya yi tsokaci game da yadda kungiyarsu ke bada gudunmawa wajen samar wa matasa aikin yi da kuma matsalolin da take fuskanta. Ga yadda hirar ta kasance: Aminiya: […]
Alhaji Adamu Musa shi ne Shugaban kungiyar masu sayar da rake a Jihar Bauchi. A cikin tattaunawarsa da wakilinmu a ofishinsa da ke Bauchi a ranar Lahadi, ya yi tsokaci game da yadda kungiyarsu ke bada gudunmawa wajen samar wa matasa aikin yi da kuma matsalolin da take fuskanta. Ga yadda hirar ta kasance:
Aminiya: Za mu so ka fara gabatar da kanka?
Adamu Musa: Sunana Alhaji Adamu Musa Shugaban kungiyar masu sayar da rake na Jihar Bauchi, na yi fiye da shekara 35 ina sayar da rake. Na gaji sayar da rake daga iyayena. A yau kuma ni ne shugaban kasuwar rake a nan Bauchi.
Aminiya: Wadanne matsaloli kungiyarku take fuskanta?
Adamu Musa: kungiyarmu tana da dimbin matsaloli, misali muna bukatar gwamnati ta kewaye mana wannan kasuwa, sannan ya kamata gwamnati ta fahimci cewa wannan kungiya tana daya daga cikin tsofaffin kungiyoyi masu tarihi a Jihar Bauchi. Mambobin kungiyarmu sun zarce sama da dubu uku, kuma mun yi wa kowane mamba takardar shaida, masu talla a baro kowa yana yawo da kwando, kuma duk karshen wata muna shiga aikin tsaftace muhalli na gwamnatin Jihar Bauchi.
Sakamakon matsalar tsaro da ake fuskanta a jihohin Najeriya duk wanda ya zo shiga wannan kungiya sai mun masa binciken kwakwaf kafin mu masa rijista. Akwai jami’an tsaro wadanda muke aiki tare a wannan kasuwa ta ’yan rake. Nan da wani lokaci za mu tsunduma cikin harkokin siyasa domin tafiya da zamani, sai dai za mu yi taka tsan-tsan saboda yanayi.
Aminiya: Ko sayar da rake na iya daukar nauyinku?
Adamu Musa: Wannan sana’a ta sayar da rake ta yi mini komai a rayuwa, tun lokacin da na tashi nake rike da sana’ar hannu biyu, kuma Allah Ya rufa mini asiri, muna ci, muna sha, muna kuma tallafa wa iyaye. Ina kuma tabbatar maka da cewa wannan sana’a ta fi aikin gwamnati rufin asiri a rayuwa, don haka ni da wannan sana’a mutu-ka-raba. Kuma da yawa daga cikin mambobin wannan kungiya matasa wadanda suka fito daga jihohi daban-daban na Najeriya, suna amfana da wannan sana’a.
A wannan sana’a wasu sun gina gidaje, wasu sun mallaki motocin hawa da na haya, haka wasu suna kiwon shanu da sauransu, saboda haka muna alfahari da wannan sana’a.
Aminiya: Mene ne sakonka ga matasan da ke zaman kashe wando?
Adamu Musa: Sakona ga matasa shi ne, don Allah su kama sana’a, domin ita ce take kara wa mutum mutunci a idon al’umma, babu wata al’umma da za ta samu ci gaba mai amfani dole sai da zaman lafiya da kwanciyar hankali. Kuma don Allah a yi hakuri da kadan, domin babu wani mutum a duniya wanda zai samu ci gaba, dole sai ya fuskanci tarin matsaloli da kalubale. Ba na kaunar in ga matashi mai koshin lafiya ba shi da wani aiki sai yawon roko a wurin ’yan siyasa.
Daga karshe ina kira ga mambobin wannan kungiya su kasance masu bin doka da oda a koyaushe. Sannan su rika bin dokokin hukuma a lokacin da suke talla a cikin gari.