Sayar da takalma akwai riba idan an yi hakuri – Mustapha Umar
Aminiya: Ko za ka gaya mana yadda wannan sana’a ta sayar da takalma take? Shugaba Mustafa: To farko dai ita sana’ar takalma sana’a ce ta saye da sayarwa. Ba mu ne ke yin takalman ba, muna sayowa daga wajen manyan dillalai ne mu kasa mu rika sayarwa kai tsaye ga masu amfani da su. Sana’a […]

Aminiya: Ko za ka gaya mana yadda wannan sana’a ta sayar da takalma take?
Shugaba Mustafa: To farko dai ita sana’ar takalma sana’a ce ta saye da sayarwa. Ba mu ne ke yin takalman ba, muna sayowa daga wajen manyan dillalai ne mu kasa mu rika sayarwa kai tsaye ga masu amfani da su. Sana’a ce mai bukatar dan karamin jari da farko, amma in mutun ya yi hakuri da za ta zama mai babban jari. A da can ba kowane ke yinta zalla ba, ana hadawa da wasu sauran kayan kasuwar. A hankali sai aka fara gane ashe kasuwa ce mai zaman kanta ba sai ta rabu da kowa ba. Kuma a da muna yawo tsakanin kasuwanni da garuruwa, amma daga baya sai muka fara tattaruwa waje daya.
Aminiya: Tsawon wane lokaci kuke gudanar da kasuwancin takalma a nan?
Shugaba Mustafa: Sama da shekaru 20 muna gudanar da wannan sana’a ta sayar da takalma a nan bakin tsohuwar ma’aikatar watsa labarai da ke kusa da babban masallacin jumma’a, wanda da muna zuwa ne a lokuttan gabatar da bukukuwan salla, walau ta bayan azumi ko kuma babbar salla, wadda ake yin layya. Ma’ana muna zuwa sau biyu a shekara. To da muka ga yadda jama’a suka karbe mu ta hanyar sauki da muke yi ga jama’a, sai muka nemi alfarma wajen Magajin Garin Katsina, wanda yake shi ne Sarkin Katsina a yanzu, wato Alhaji Abdulmuminu Kabir Usman da a ba mu dama mu cigaba da gudanar da wannan sana’a tamu a nan, kuma Allah cikin ikonSa ya ba mu wannan dama. Sannan muka nemi hadin kan wadannan ma’aikatu da muke makwaftaka da su a nan ma ba mu samu wata matsala ba. Da haka wannan wuri ya cigaba da bunkasa har muka fara janyo abokan sana’armu ’yan jiha. Abu dai ya cigaba da yaduwa.
Aminiya: Ke nan a daidaiku kuka fara zuwa ba a kungiyance ba?
Shugaba Mustafa: Haka ne domin a hankali muka fara zama. To lura da cewa zamani na tafiya wanda ta kai komai kuke yi in ba a kungiyance ba da wuya a samu nasara a kai,wannan ne ya sanya muka kafa wannan kungiya tamu mai suna,”Nasiha” wato kungiyar Nasiha ta masu sayar da takalma, mun kuma yi mata rajista a cikin watan Janairu na 2013. Mun kuma sanya wannan suna ne ta lura da irin yadda muke gudanar da sana’armu a wajen, saboda takalmin da za ka sayo a kasuwa a kan Naira dubu mu za mu sayar da shi a Naira 800. Kuma iri daya ne da wancan na Naira dubun.
Aminiya: Ya zuwa yanzu kuna da membobi kamar nawa?
Shugaba Mustafa: Mun kai mutun 60 ko 70 ban da wadanda suke zuwa sauran wasu kasuwannin. Kuma wasu na kara shigowa.
Aminiya: Yaya ita wannan sana’a take?
Shugaba Mustafa: To gaskiyar magana sana’ar sayar da takalma sana’a ce mai rufin asiri, wadda kuma take taimakawa a wajen hana zaman banza. Kuma sana’a ce mai kawo riba in dai aka yi hakuri. Misali, ka je ka saro takalmi a ce akan Naira 700 duk taki daya, sanya kudin mota da na abinci, za ka sayar a kan Naira dubu ko dubu 1,200 ko 1,300. To ina laifin abin da aka dan samu? Kuma cikin ikon Allah da wuya ka fito ba ka samu wanda ya sayi koda guda daya ba ne. In kuwa aka ce lokacin wani biki ne misali, na salla ko wata hidimar, to muna iya kai har karfe sha biyun dare ana huldar ciniki.
Aminiya: In na fahimce ka ka ci moriyar sana’ar
Shugaba Mustafa: Fadi barnar zance, domin duk wani abin biyan bukata na rayuwa wannan sana’ar ta yi mini. Ina ci, ina sha tare da iyalina a cikinta har ma in taimaka wa wasu. Kuma ka ganmu nan har yau babu wanda ya je banki ko wajen wani domin cin bashi. Allah ya rufa mana asiri.
Aminiya: To ina maganar kawo kayan?
Shugaba Mustafa: Ana kawo kaya. Sai dai kuma a yanzu ba kamar da ba saboda a yanzu har da takalman da ake yi a nan gida Katsina muke sayarwa kuma jama’a sun karbe su sosai kamar yadda suka karbi na waje, saboda an gane ingancinsu da kuma karko. Inma ba an nuna maka ba wani takalmin ba ka iya bambance da na wajen.
Aminiya: Kasan ana kafa kungiya ne don cimma wata manufa, mene ne kudurinku?
Shugaba Mustafa: Kawo sauki ga jama’a shi ne babbar manufar wannan kungiya, sai kuma tallafa wa kanmu da kanmu a lokacin da bukatar neman wani tallafi da mutananmu za su nema walau ta fuskar sana’ar ko wata lalurar daban. Sannan muna da kudurin kawar da zaman kashe wando a tsakanin matasa. Ga dai shaida nan a gabanka, baya ga ’ya’yanmu har da na wasu. Kuma sai mun tantance kafin mu barka ka fara mu’amulla da mu.
Aminiya: To ina maganar matsaloli?
Shugaba Mustafa: To babbar matsalarmu dai bai wuce karancin jari ba,wanda in da za mu samu to kamar yadda gwamnati take tallafa wa sauran kungiyoyi to muma a sanya mu a jerin wadanda za su ci gajiyar shirin. Ko ba komai dai wannan gwamnati ta Masari mun ga tana iya nata na tallafawa wajen kashe zaman banza,kuma har wurare ta kebe na koyar da sana’o’i wanda takalma na cikin abin da ake koyarwa. Ashe in an lura mu ne kashin bayan cigaban waccan sana’ar domin mune masu dauka mu kai a masaya har jama’a su gani su saya. Sai abu na biyu shi ne muhalli. A yanzu dai bakin titi muke kuma wuri kurarre,amma da zamu samu inda za’a bamu fili da harkar kasuwanci ta kara fadada,domin har shigowar baki za a kara samu domin ita kasuwa dole sai da baki. Sannan akwai wata babbar matsalar akan wannan kasuwar wato daukewar ciniki na tsawon wani lokaci bama kamar irin wannan halin da muke ciki na matsin tattalin arziki. Sai dai kuma ina so in yi amfani da wannan dama inyi kira ga su ’ya’yan wannan kungiya da su cigaba da ba kungiya hadin kai, kuma su zamo masu gaskiya a wajen gudanar da sana’ arsu da sauran harkokinsu na yau da kullum. Ita kuma gwamnati muna rokon da dube mu da idon rahama ta samarwa wannan kungiya da muhalli wanda wata rana za’a tarar wajen ya koma wata babbar kasuwa ko babbar masana’antar yin takalma.