Sayar wa Dangote danyen mai: ’Yan Arewa sun yaba da matakin

NNPC ya dauki gabarar sayar wa Matatar Dangote danyen mai da take bukata a kan kimanin Dala biliyan 13.5 a shekara

Sayar wa Dangote danyen mai: ’Yan Arewa sun yaba da matakin

Masana daga yankin Arewa sun yaba da matakin da Gwamnatin Tarayya ta dauka na sayar wa Matatar Dangote da danyen mai a kan farashin Naira.

Kungiyar Kwararrun Arewa (ATT) ta jinina wa Shugaban Tinubu bisa daukar matakin ickin kimanin awa 24 bayan kungiyar ta nemi ya dauki dakile yunkurin yi wa matatar zagon kasa.

Shugaban ATT, Muhammad Alhaji Yakubu tare da jagoran kungiyoyin fararen hula, Rabaran Nicholas Daniel Jatau, a cikin sanarwarsu ta gwiwa sun ce abin da shugaban kasan ya yi ya nuna shi mai sauraron jama’a ne.

“Mun fahimci cewa makasudin umarnin shugaban kasa shi ne samun daidaito a farashin mai da kuma na canjin dala, shi ya sa Majalisar Zartaswa ta Kasa ta amince da bukatarsa ta sayar wa Matatar Dangote danyen mai da Naira.

“Abin yabawa ne yadda kamfanin NNPC ya dauki gabarar ba wa matatar jiragen ruwa hudu na danyen mai daga cikin 15 da take bukata a shekara a kan Dala biliyan 13.5.

“Muna jinjina ga shugaban kasa bisa kafa Hukumar Kula da Cigaban Arewa ta yamma, wadda muke sa ran za ta bunkasa cigaban yankin,” in ji shanarwar.

Ta kara da jinjina kan dokar karin mafi karancin albashi zuwa N70,000  da shugaban kasan ya rattaba wa hannu, da cewa “alama ce ta cewa nan gaba za a samu sauki a kasar nan.

“Muna kuma gargadin kasashen Amurka da Birtaniya da Kanada bisa gargadin tsaro da suke aika wa ’yan kasashensu da ke Najeriya game da yiwuwar barkewar tarzoma a zanga-zangar da ke tafe a fadin kasar nan.

“Hakan da suke yi ba komai ba ne face razana matafiya, alhali al’ummar Najeriya na ci gaba da gudanar da harkokinsu kalau duk kuwa da zanga-zangar da ta riga ta kawo jiki,”  in ji su.

Sibil Difens ta kama mutum 10 kan aikata laifuka daban-daban a Gombe

’Yan sanda sun kama ’yan fashi 6 a Gombe

Mata sun yi zanga-zanga gabanin rantsar da Trump a Amurka

TikTok ya daina aiki a Amurka