Sayen katin zabe asara ne -Hukumar zabe

Mista Nick Dazan shi ne mukaddashin Darakta a Hukumar zabe ta kasa (INEC) mai kula da bangaren ilmantar da masu kada kuri’a da kuma yada labarai, ya yi wa  Aminiya bayani a kan mataki da hukumarsu ta kai wajen samar da katin zabe na dindin zuwa yanzu da kuma dalilin dogewarta a kan cewa  sai […]

Sayen katin zabe asara ne -Hukumar zabe

Mista Nick Dazan shi ne mukaddashin Darakta a Hukumar zabe ta kasa (INEC) mai kula da bangaren ilmantar da masu kada kuri’a da kuma yada labarai, ya yi wa  Aminiya bayani a kan mataki da hukumarsu ta kai wajen samar da katin zabe na dindin zuwa yanzu da kuma dalilin dogewarta a kan cewa  sai ta yi amfani da katin da kuma na’urar tantance masu zabe:

Aminiya: Sai ka gabatar da kanka

Nick Dazang: Sunana Nick Dazang, ni ne mukaddashin darakta a bangaren ilmantar da masu kada kuri’a da kuma yada labarai na hukumar zabe ta kasa.
Aminiya: Zuwa yanzu wane adadi kuka kai wajen raba kuri’a na dindindin?
Nick Dazang: Adadin wadada suka amshi katin zabensu zuwa ranar Talatar nan, kamar yadda na samu bayani daga sashinmu na kundin bayanai na I.C.T, ya nuna cewa wadanda suka amshi katinsu na dindin wato P.b.C ya kai kashi 75 cikin dari, wanda ke matsayin mutane miliyan 52 da dubu 233 da 396 ke nan, daga cikin mutane miliyan 69 da aka yi wa rajista. Wannan adadi yana karuwa a kullum, saboda mun aike da daukacin katin zuwa jihohi har zuwa mataki na gundumomi, ya kuma kunshi na daukacin wadanda muka yi wa rajisata wadanda katunansu suka kone ko suka salwanta ta hanyoyi daban-daban, ko kuma wadanda suna da katin wanda aka yi amfani da shi a baya, duk mun yi masu sabbin kati a wannan tsari na kati na dindindin.
Aminiya: Yaya batun wadanda sai yanzu suka samu zarafin zuwa yin rajistar, ko akwai tanadin ci gaba da yi masu a wannan kari na kwanaki da kuka yi?
Nick Dazang: A gaskiya ba sa cikin wannan karin da muka yi a yanzu, mun kauce wa hakan ne don gudun kada a sake fadawa wata sabuwar matsala, kuma da ma a ka’ida shi ne za a dakatar da yin rajista kwana 30 gabanin yin zabe, to a dalilin hakan mun dakatar da ci gaba da yi wa mutane rajista tun a ranar 13 ga watan Janairu, kasancerwar a baya an tsara za a yi zabe na farko ne a ranar 14 ga watan Fabarairu, to ko da muka kara lokaci a yanzu ba mu dawo da batun yin rajista ba, sai dai bada kati kadai ga wadanda suka riga suka yi.
Aminiya: Wadansu na kira da a ba da damar yin zabe da katin na wacin gadi, ga kuma masu bukatar a janye amfani da na’ura mai tantance katin zabe, mene ne dalilin dogewarku da sai an yi amfani da wadannan tanadi?
Nick Dazang: wannan abu ne wanda ba zai yiwu ba, saboda wannan tsarin na kunshe ne a cikin dokar zabe ta 2015, sannan mun yi yarjejeniya a tsakaninmu da jam’iyyun siyasa a kan da wannan katin ne za a yi zabe da shi kuma sai an tantance. Na biyu kuma a sakamakon fahimtar da muka samu a kan hakan, mun shirya tsarin zabenmu a kan hakan, inda aka kashe kudi mai yawa a kai. Na uku a shekarar zabe ta 2011 an samu matsala ta yin rajista fiye da sau daya, wanda adadinsu ya kai har miliyan 2, ka ga ke nan idan muka amince da bukatarsu ta janye amfani da wannan tsarin bayan mun yi nisa a ciki, wanda hakan na nufin bada kafar yin zabe ke nan fiye da sau daya tare da bada damar yin magudi ta wadansu hanyoyi, alhali burinmu shi ne mu aiwatar da zabe ingacecce. Wannan shi ne dalilin dogewarmu a kai, kuma a kai muke ba za mu yarda da wani tsari da ya gaza hakan ba.
Aminiya: A wannan karin kwanaki da kuka yi akwai korafin cewa kun janye bada kati a wurare da dama.
Nick Dazang: Dama kwana uku muka ware don raba katin dindindin a daukacin cibiyoyin zabe, bayan nan za a ci gaba da raba katin ne a matakin gunduma kadai, a kan hakan muke a yanzu. Za mu ci gaba da bayar da kati har zuwa ranar 8 ga watan Maris, katin nan kuma suna jibje a wadannan wurare, jami’anmu jira kawai suke yi masu katin su je su amsa.
Aminya: Haka nan akwai wadanda ke korafin cewa kun fifita wadansu jihohi a kan wadansu.
Nick Dazang: Ba batun nuna bambanci ko fifiko a tsarin rabon katin dindindin. Sai dai gaskiyar al’amari shi ne, wadannan jihohi da suke magana a kai su ne a gaba wajen yin rajistan zabe, wato jihohin Legas da Kano da Kaduna, da dai sauransu. Babu wanda aka nuna wa fifiko ko ba su kati na musamman, kuma umarni da muka bai wa jami’anmu shi ne, su tabbata kowa ya karbi katinsa da kansa ba sako ba, sannan a rubuta sunansa da lokacin da ya karba. Sannan idan ka duba, yawancin jihohin da aka samu tangarda a wajen raba wannan kati, jihohi ne da ke a rukuni na uku, wadanda kuma yawancinsu suna Arewa ne. Wadannan jihohi sun hada da Kaduna da Katsina, wajen sau uku muna dage raba bada kati a wadan nan jihohi, sai dai mun tuntubi masu ruwa da tsaki a al’amuran zabe na wadannan jihohi wajen sanar da su matsalar don bai wa jama’arsu hakuri, wannan ko ya faru ne a sakamakon tsaiko da aka samu daga bangaren dan kwangila da muka bayar a nan Najeriya. Sai dai daga bisani ya inganta buga katin daga dubu 300 zuwa dubu 650 a duk yini, sai kuma aikin da muka bai wa wani kamfani a kasar China, wanda shi kuma yake buga kati miliyan 1 da dubu 400 a duk yini, har dai muka samu muka kammala buga daukacin wadan nan kati na dindindin kuma tuni aka aika da su zuwa jihohi da mataki na gundumomi. Idan ma akwai korafi to jihohi da ke cikin rukuni na uku su ne ya kamata su yi, saboda wannan matsala su ne ta shafa. Jihohi sun hada da Kano da Kaduna da Katsina da Neja da Filato da Ribas da Legos da kuma Imo. Wadannan jihohi su ne suka fi yawan wadanda muka yi wa rajista, wadanda yawan jama’arsu da suka yi rajista ya ninka na jihohi da ke rukuni na daya ko rukuni na biyu.
Aminiya: Akwai bayanai da ke cewa wadansu na zagayawa suna sayan katin jama’a, wane mataki kuka dauka a kai?
Nick Dazang: Lallai mun samu wannan bayani kuma muna nan muna sa ido a kai, kuma muddin muka kama wani da hakan za mu mika shi ga jami’an tsaro don daukar matakin da ya dace da shi. Haka nan muna fadakar da jama’a a kan kada su yarda su sayar da katinsu. Sai dai a sani, daukar bayanan kati da niyyar buga na boge da ke dauke da bayanansa ba zai yi aiki ba, saboda idan ka zo da na boge ko da yana dauke da bayanan da katin da ka kwaikwaya na’urarmu za ta fallasa ka. An yi mata tsari ta yadda kana tahowa daga tazarar mita biyar za ta fara sunsunaka tare da katinka, sannan kazo ka mikata ka dangwala yatsarka, sannan ta yi bayani ta lasifika kowa na ji, ta ce, “wannan shi ne mai katin, ko kuma ba shi ne mai katin ba.”
Aminiya: Wane tanadi kuka yi wa ’yan gudun hijira?
Nick Dazang: A gaskiya mun samu kanmu a cikin halin tsaka mai wuya a game da ’yan gudun hijira, saboda wannan shi ne karo na farko da muke yin zabe a cikin wannan hali. Sai dai duk da haka mun yi wa ’yan gudun hijira da ke cikin jihohi uku da da dokar ta-baci ta shafa rajista. Wannan tanadi ta hadin gwiwa ce a tsakaninmu da gwamnatocin jihohin, inda za a yi musu rajista a wurarensu na gudun hijira, a ba su katinsu na dindindin. Sannan idan lokacin zabe ya yi, su jihohin nan ne za su dauki nauyin daukarsu daga inda suke zuwa inda ake ganin ya dace a yi musu zabe, idan akwai halin zaman lafiya da kwanciyar hankali. Kuma mun bi wannan tsarin ne bayan tuntubar kwararru tare da bin tsarin da aka bi a wadansu kasashe na duniya inda irin wannan matsala ta auku. Sai dai wannan ya tsayane a jihohi ukun nan kawai, ban da sauran jihohi da matsalar ’yan gudun hijira ta shafa. Hakan kuma ya faru ne a sakamakon rashin sanin takamammen adadin ’yan gudun hijira da ke wadansu jihohin, sannan kuma ga kurewar lokaci.