Sayen kuri’a: EFCC ta kama tsabar kudi N32.4m a Legas

Ana zargin kudaden na sayen kuri’a ne

Sayen kuri’a: EFCC ta kama tsabar kudi N32.4m a Legas

Sabbin-takardun-kudi

Jami’an Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC), sun kama haramtattun kudaden da suka kai Naira miliyan 32.4 a Legas wanda ake zargin an tanade su ne domin sayen kuri’a yayin zaben da zai gudana ranar Asabar.

Jam’ian sun kama kudin ne yayin da suke gudanar da aikinsu a jihar don yaki da sayen kuri’a a lokacin zabe.

Bayanai  sun nuna an cafke mutum guda wanda ba a bayyana ko wane ne ba da hannu wajen rabon kudin, Inda aka tafi da shi domin zurfafa bincike.

Wannan na zuwa ne kasa da sa’o’i 24 bayan da makamancin haka ya auku a Jihar Ribas inda ’yan sanda suka cika hannu da dan Majalisar Wakilai, Chinyere Igwe, a Fatakwal dauke da tsabar kudi $498,100.

Cikin sanarwar da ya fitar, Kakakin EFCC,  Wilson Uwujaren, ya ce Shugaban Hukumar na Kasa, Abdulrasheed Bawa, ya bukaci baki dayan jami’an da aka tura aikin zabe da kada su ba da kafa ko kadan ta yin ta’ammali da kudi yayin zaben.

Ya ce sun baza jami’ansu a ko’ina a fadin kasar nan domin hana batun sayen kuri’a a wajen zabe.

Haka nan, ya ce za ayi amfani da duk hanyoyin da hukumar ta sahale wajen kai rahoton duk wanda aka gani yana harkar sayen kuri’a yayin zabe.

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50