Sayen motocin sulke na Naira miliyan 255: ’Yan Najeriya sun fusata da Ministar Sufurin Jiragen Sama

Sayen motocin masu sulke guda biyu kan Naira miliyan 255 da Ministar Sufurin Jiragen Sama Mis Stella Oduah ta yi, ya fusata ’yan Najeriya, wadanda kashi 60 daga cikinsu suke rayuwa kasa da Naira 160 a kullum. Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Najeriya (NCAA), ta ce ta sayo motocin kirar BMW 760 Limousines […]

Sayen motocin sulke na Naira miliyan 255: ’Yan Najeriya sun fusata da Ministar Sufurin Jiragen Sama

Stellah Oduah Ministar Zirga-Zirgar Jiragen SamaSayen motocin masu sulke guda biyu kan Naira miliyan 255 da Ministar Sufurin Jiragen Sama Mis Stella Oduah ta yi, ya fusata ’yan Najeriya, wadanda kashi 60 daga cikinsu suke rayuwa kasa da Naira 160 a kullum. Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Najeriya (NCAA), ta ce ta sayo motocin kirar BMW 760 Limousines kan Naira miliyan 255 wata biyu da suka gabata bayan da Ministar ta bukaci haka, bisa hujjar tsaro.
Darakta Janar na Hukumar NCAA Fola Akinkuotu ya shaida wa manema labarai a karshen mako cewa, “Al’ada ce a duk duniya mu dauki ministarmu da… manyan baki ’yan kasashen waje a mota mai sulke a duk lokacin da suka zo Najeriya.
A makon jiya ne wata majiya ta ballo wa Ministar liki, yayin da magoya bayanyta suka ce wani yunkuri ne na bata mata suna. Sai dai galibin ’yan Najeriya da suka gaji da facakar ’yan siyasa ta sayen motoci da gidajen alfarma da kuma zuwa asibitocin kasashen waje da kai ’ya’yansu makarantun waje sun rika Allah wadai da fusata da lamarin.
kungiyar Network for Enbiroment and Economic Justice ta nemi Minista Oduah ta yi murabus inda ta ce: “A lokacin da ’yan Najeriya ke cikin kuncin talauci, rashin kan gado ne a yi amfani da wannan tsugugun kudi wajen sayo motoci ga Ministar.”
Kakakin Oduah Joe Obi ya fadi a ranar Litinin cewa ana bukatar motocin ne sakamakon “yadda ta bayyana a fili ana barazana ga rayuwarta.”
Mutane da dama suna zargin an yi zurmuken kudin motocin, inda suka ninka sau kusan hudu kan farashinsu a sauran kasashe.
Misis Oduah, wadda ta hannun damar Shugaba Goodluck Jonathan a cikin wannan wata ta fusata iyalan wadanda hadarin jirgi ya rutsa da su, inda ta ce yin Allah ne.
Sakamakon fusatar ’yan Najeriya Majalisar Tarayya ta umarci kwamitinta na sufurin jiragen sama ya binciki batun tare da duba yadda aka yi cinikin, wanda aka ce ba ya ma cikin kasafin ma’aikatar na bana.
A ranar Talata Kakakin Ma’aikatar Sufurin Jiragen Sama Yakubu Datti ya sanya siyasa cikin lamarin inda ya zargin ’yan adawa kan kiran Ministar ta yi murabus a wani yunkuri na hana Shugaba Jonathan sake neman takara a zaben 2015.
Da farko lokacin da labarin ya bayyana Datti ya ce zargin jita-jita ce kawai, domin Misis Oduah tana da dukiyar da ba sai ta sanya wata hukuma da ke karkashinta ta saya mata motoci ba.
A yayin da majalisar ta ce a binciki lamarin wata majiya ta ce Shugaba Jonathan ya aika wa Ministar takardar tuhuma kan badakalar, kuma a shekaranjiya Laraba, Kakakinsa Rueben Abati ya ba da sanarwar cewa Shugaba Goodluck Jonathan ya kafa kwamitin da zai binciki sayen motocin sulken da Minista Oduah ta yi.