Schick ya yi ritaya daga buga wa Jamhuriyar Czech tamaula
Schick ya yi fice musamman a Gasar Euro 2020, inda ya zama ɗan wasa mafi cin ƙwallaye tare da Cristiano Ronaldo
Ɗan wasan gaba na Jamhuriyar Czech, Patrik Schick, ya sanar da yin ritaya daga buga wa ƙasarsa tamaula.
Wannan dai na zuwa ne sa’o’i kaɗan bayan Czech ta fice daga Gasar Kofin Duniya ta 2026 bayan shan kashi da ci 3-0 a hannun Mexico.
- ’Yan bindiga sun kashe tsohon shugaban APC a Kebbi
- An haramta shan barasa saboda tsananin zafin rana a Paris
Schick mai shekara 30, wanda ke taka leda a Bayer Leverkusen, ya buga dukkan wasannin rukuni uku na Czech a gasar, amma bai samu nasarar zura ƙwallo ko ɗaya ba, yayin da tawagar ta samu maki ɗaya kacal bayan kunnen doki da ta yi a wasan rukunin A da ta fafata da Afirka ta Kudu.
Tun bayan fara buga wa Czech wasa a shekarar 2016, Schick ya zura ƙwallaye 26 a wasanni 56 da ya buga wa tawagar ƙasar.
A cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Instagram, Schick ya ce bayan dogon nazari ya yanke shawarar yin ritaya daga wasan ƙasa da ƙasa
“Yau ne ƙarshen aikina na buga wa ƙasar Czech tamaula. Wannan ba shawara ce ta gaggawa ba, domin na daɗe ina tunani a kanta,” in ji shi.
Schick ya fara taka leda ne a Sparta Prague kafin ya buga wa Sampdoria da AS Roma da RB Leipzig tamaula, sannan ya koma Bayer Leverkusen a shekarar 2020.
Ya yi fice musamman a Gasar Euro 2020, inda ya zama ɗan wasa mafi cin ƙwallaye tare da Cristiano Ronaldo bayan kowannensu ya zura ƙwallaye biyar a gasar.
Ɗaya daga cikin fitattun ƙwallayensa ita ce wadda ya ci Scotland daga kusan mita 50, ƙwallon da ta shiga tarihi a Gasar Euro 2020.
Schick ya ce yana barin tawagar ƙasar cike da alfahari dangane da abubuwan da ya cimma, amma yana da yaƙinin cewa ƙwallon kafar Czech na buƙatar gyara.
“Ina alfahari da abin da na cimma sanye da rigar Czech, amma ina ganin ƙwallon kafar ƙasar na iya yin fiye da yadda take yi a yanzu. Akwai abubuwa da dama da ya kamata a sauya,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa babu wata nasaba ta fushi ko takaici da ta sanya shi bayyana wannan ra’ayi, sai dai don kishin da yake yi wa ci gaban ƙwallon ƙafar ƙasarsa.