SDP ta tsayar da mata 11 takara a Jihar Neja
Jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) ta tsayar da mata 11 da za su fafata takara a kujeru daban-daban da suka fara daga Majalisar Jiha da ta Tarayya da na Gwamna. Shugaban Jam’iyyar Alhaji Alfa Muhammad ya shaida wa wakilinmu haka a Minna, inda ya ce, “Maganar da nake da kai yanzu, mace ce za ta […]
Jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) ta tsayar da mata 11 da za su fafata takara a kujeru daban-daban da suka fara daga Majalisar Jiha da ta Tarayya da na Gwamna.
Shugaban Jam’iyyar Alhaji Alfa Muhammad ya shaida wa wakilinmu haka a Minna, inda ya ce, “Maganar da nake da kai yanzu, mace ce za ta tsaya mana takarar Gwamna, kuma muna da mata biyu da za su tsaya takarar Sanata, akwai na Majalisar Wakilai da ta Dokokin Jihar. Duk sun cika sharuddan da Hukumar Zabe ta gindaya wa masu sha’awar tsayawa takara,” inji shi.
Shugaban Jam’iyyar ya ce sun yi la’akari da irin gudunmawar da mata suka dade suna ba kasar nan a matakai da dama shi ya sa suka ba su damar gwada sa’ar da za su wakilci jama’arsu a matakan da suka kamata don su samu ingantacciyar rayuwa.
Ya bayyana gamsuwa kan yadda jama’a ke tururuwa don yin rajista da jam’iyyarsu.
Shugaban ya ce, “A yanzu haka mun bude ofisoshi da jama’a ke zuwa don ganawa da jama’anmu a kananan hukumomi 22 daga cikin 25 da ke wannan jihar. Kuma za mu bude ofisoshi a kananan hukumomin Agaye da Agwara da na Mashegu kafin a zaben da ke tafe.”
Shugaban ya ce jam’iyyarsu ce za ta kwace gwamnati daga hannun Jam’iyyar PDP, kuma ta samu rinjaye a majalisar jihar da tarayya, inda tuni suka fara tattaunawa da wasu manyan ’yan siyasa domin dawowa jam’iyyarsu.