Seaman Abbas da Hussaina: An dakatar da shirin Brekete Family Hausa
Rikice-rikicen da suka biyo bayan damabrwar Seaman Abbas da Hussaina, Ordinary President ya daina gabatar da shirin Brekete Family da harshen Hausa.
Rikici ya ɓarke tsakanin Seaman Abbas da matarsa Hussaina, da kuma mai gabatar da shirin nan na Brekete Family, Ahmad Isa da aka fi sani da Ordinary President.
Rikicin ya fara ne bayan Hussaina ta fitar da wani bidiyo tana cewa mijinta na yi mata duka, saboda zargin ta da yake da sama da faɗi da wasu kuɗaɗe da mota da aka ba su a matsayin tallafi.
A bidiyon ta kuma bayyana cewa tsangwamar ba ga iya shi ta tsaya ba, har na danginsa, abin da ta ce ya yi sanadiyar komawarta gidan iyayenta.
To sai dai mijin nata ya fito ya musanta zarge-zargen, inda ya ce suna zaune lafiya, hasali ma ta je ganin gida ne bayan rashin lafiyar da ta yi.
Shi ma dai Ordinary President da ake zargin ya hana su Seaman ɗin tallafin Naira Miliyan 20 da Gwamnan Kaduna, Uba Sani ya ba su, ya ce zance ne mara tushe balle makama.
Ya bayyana cewa a sakamakon waɗannan rikice-rikicen da suke ɓullowa a lamarin Usaina, ya daina gabatar da shirin Brekete Family da harshen Hausa.