SEMA ta tallafawa jama’ar Kaura da aka kaiwa hari

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Kaduna (SEMA) ta kaiwa jama’ar da harin wasu ‘yan bindiga ya rutsa da su a gundumar Zangan da ke Karamar hukumar Kaura ta jihar Kaduna. Yayin da ta ke mika tallafin ga shugaban Karamar Hukumar, shugabar hukumar ta SEMA HajiyaMaimunatu Asabe Abubakar, ta ce bisa la’akari da abubuwan […]

SEMA ta tallafawa jama’ar Kaura da aka kaiwa hari

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Kaduna (SEMA) ta kaiwa jama’ar da harin wasu ‘yan bindiga ya rutsa da su a gundumar Zangan da ke Karamar hukumar Kaura ta jihar Kaduna.

Yayin da ta ke mika tallafin ga shugaban Karamar Hukumar, shugabar hukumar ta SEMA HajiyaMaimunatu Asabe Abubakar, ta ce bisa la’akari da abubuwan tausayin da suka faru da kuma halin da wadanda harin ya shafae su ke ciki musamman mata da kananan yara ya sa hukumar su tayi gaggawan kawo dauki don saukaka musu halin da suka tsinci kansu a ciki.

Hajiya Maimuna, ta bayyana harin a matsayin abin takaici, tayi kira ga mutanen yankin da su zauna lafiya da junansu duk da irin bambamcin addini da kabila da su ke da shi.

 

Yayin da yake jawabi bayan karbar kayayyakin, shugaban karamar hukumar Dakta Katuka Ayuba Bege, ya yabawa hukumar ta SEMA bisa ga abin da ya bayyana da daukin gaggawa a lokacin da ya dade, inda ya yi alkawarin mika kayayyakin ga jama’ar sa abin ya shafa.

Ya ce, Karamar Hukumar ba za tayi kasa a gwiwa ba wajen ganin ya hada kai da kwamitin zaman lafiya ta jihar Kaduna don shiga tsakanin lamarin don samun kyakkyawa fahimtar juna tsakanin mutanen Ganawuri da ke jihar Filato da kuma al’ummar Fulani da Attakat da ke Zangan a jihar Kaduna.

Kayayyakin da aka raba sun hada da katifu da barguna da gidajen sauro da buhunan shinkafa galullukan man ja da katon-katon na taliyar indomi.

Lokacin mika tallafin