Senegal: Kasar Afirka ta farko da ta ketare zuwa zagayen ’yan 16 a Gasar Kofin Duniya

Kocin Senegal Aliou Cisse, ya yi alkawarin kafin wasan cewa kwararrun ’yan wasansa ba za su sassauta ba, kuma ’yan Afirka ne suka nuna bajinta.

Senegal: Kasar Afirka ta farko da ta ketare zuwa zagayen ’yan 16 a Gasar Kofin Duniya

Senegal’s supporters celebrate in Dakar on February 6, 2022 the victory of the Africa Cup of Nations (CAN) 2021 final football match against Egypt. (Photo by SEYLLOU / AFP)

Senegal ce kasa ta farko a duk fadin nahiyyar Afirka da ta tsallake zuwa zagayen ’yan 16 a Gasar Kofin Duniya da ake fafatawa yanzu a haka a kasar Qatar.

Haka kuma, ta tabbata cewa Senegal za ta yi gumurzunta ne a zagayen na gaba da tawagar Three Lions ta Birtaniya, wadda ita ma ta yanki tikitin ketarewa zuwa zagayen na gaba a babbar gasar tamaular.

Yadda Senegal ta kaya a wasanninta uku na rukuni

Wasa na farko:

Kwallaye biyu da aka zura dab da za a tashi a wasa, sun bai wa Netherlands damar casa zakarun Afirka, Senegal, a ranar Litinin, 21 ga watan Nuwamba, 2022.

Wannan nasara dai ta bai ’yan wasan Louis van Gaal damar fara buga Gasar Kofin Duniya a Qatar da kafar dama.

An zura kwallayen ne a wasan a minti na 84 da farawa a rukunin A, lokacin da dan wasan gaba, Cody Gakpo, ya jefa kwallon farko a ragar Senegal, kafin daga baya Davy Klaassen ya ci ta biyu a karawar.

Ana dai ganin Senegal ba za ta yi wani katabus ba saboda ta rasa tauraron dan wasanta Sadio Mane, a wasan, sakamakon rauni wato.

Kafin yanzu dai tawagar kasashen da ke rukunin A, wato rukuni na farko, an yi hasashe cewa za su tashi kunnen doki babu ci, sai dai tuni lissafi ya sauya.

Ana saura minti shida, dan wasan gaban PSV, Eindhoven Gakpo ya yi dirar mikiya a gaban golan Senegal, Edouard Mendy.

Sakamakon ya sa Netherlands ta zama ta daya a rukunin tare da Ecuador, wacce ta doke Qatar mai masaukin baki da ci 2-0 a wasan farko na ranar Lahadi, 20 ga watan Nuwamba, 2022.

Wasa na biyu:

A wasanta a biyu, Senegal ba ta yi wa masu masaukin baki Qatar sassauci ba, inda ta lallasa ta kuma tun daga nan ta tabbata cewa ta fice daga Gasar Kofin Duniya bayan sun yi rashin nasara a karo na biyu ajere.

Kasar da ke Gabas ta Tsakiya ta yi bakin kokarinta, amma ta zama tawaga ta farko da ta fice daga gasar tun a zagayen rukuni, bayan Netherlands da Ecuador sun yi canjaras 1-1 a nasu wasan na Rukunin A.

A gefe guda kuma, Senegal ta kama kasa a rukunin da makinta uku, abin da ya sa ta zama kasar Afirka ta farko da ta ci wasa a wancan lokaci.

Boulaye Dia ne ya fara jefa kwallo a ragar masu masaukin bakin minti hudu kafin a tafi hutun rabin lokaci.

Babu sani babu sabo kuma Senegal din ta sake sare gwiwar Qatar bayan Famara Diedhiou ya ci kwallo ta biyu minti uku bayan dawowa daga hutun.

Sai a minti na 78 Muntari ya farke wa Qatar kwallo daya, amma minti shida a tsakani Dieng ya kara ta uku, wadda ta sa masu masaukin bakin komawa kasan teburin rukunin ba tare da maki ko daya ba.

Wasa na uku: 

Kalidou Koulibaly ya tura Senegal zuwa zagayen ’yan 16 a gasar cin Kofin Duniya a karo na biyu kacal a tarihinta bayan nasara da ta samu a wasan da suka doke Ecuador da ci 2-1 a ranar Talata, 29 ga watan Nuwamba.

Nasarar da Netherlands ta yi kan Qatar na nufin cewa nasara ce kawai za ta taimaka wa Senegal ta tsallaka zuwa zagayen gaba a rukunin A.

Senegal ce ta fara zura kwallo ta hannun Ismaila Sarr a bugun daga kai sai mai tsaron gida.

Sai dai duk da cewa kyaftin din Ecuador Enner Valencia ya buya a wasan, dan wasan Brighton Moises Caicedo ya farke kwallon a minti na 67 kafin Koulibaly ya fitar da tawagarsa sannan Ecuador ta koma gida.

Kocin Senegal Aliou Cisse, ya yi alkawarin kafin wasan cewa kwararrun ’yan wasansa ba za su sassauta ba, kuma ’yan Afirka ne suka nuna bajinta.

Ecuador ta fara wasan a zagaye na biyu cikin karsashi sannan kuma ta kara azama, watakila tana kokarin tabbatar da cewa mamayar da Netherlands ta yi kan Qatar na nufin sai ta dage wajen yin kunnen doki don wucewa mataki na gaba.

Sai dai tuni labari ya sha banbam, yayin da Netherlands ta kawar da Qatar din daga Gasar Kofin Duniyar da take daukar nauyi, sakamakon doke ta da ta yi da ci 2-0 a karawar da suka yi ranar Talatar.

Netherlands na bukatar maki guda ne kacal kafin wasan Qatar domin zuwa zagaye na gaba, sai ’yan wasanta Cody Gakpo da Frenkie de Jong suka jefa mata kwallaye biyu da suka bata nasarar kammala wasan rukuninsu da maki 7, yayin da Senegal ta zama ta biyu da maki 6.

Sai kuma Ecuador a matsayi na 3 da maki 4, kana mai masaukin baki Qatar a matsayin na 4 ba tare da maki ko guda ba.

Ana sa ran Netherlands ta kara a zagaye na 2 da kungiyar da za ta zo ta biyu a rukunin B wanda ya kunshi kasashen Ingila da Wales da Iran da Amurka.

Senegal ce ta zo ta biyu a wannan rukunin na A da maki 6, abin da ya bata damar zama kasar Afirka ta farko da ke halartar gasar da ta samu damar zuwa zagaye na biyu.

Netherlands na daga cikin manyan kasashen da ake ganin za su yi tasiri a wannan gasar wajen zuwa wasannin kusa da na karshe.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos