Senegal ta sallami kocinta bayan ficewa daga Gasar Kofin Duniya

Matakin ya biyo bayan rashin nasarar da Senegal ta yi na kai wa zagaye na 16, bayan ta sha kashi a hannun Belgium.

Senegal ta sallami kocinta bayan ficewa daga Gasar Kofin Duniya

Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Senegal (FSF) ta sanar da sallamar kocin ƙungiyar ƙasa, Pape Thiaw, tare da ma’aikatansa bayan ficewar Senegal daga Gasar Kofin Duniya ta 2026.

Matakin ya biyo bayan rashin nasarar da Senegal ta yi na kai wa zagaye na 16, bayan ta sha kashi a hannun Belgium da ci 3-2, duk da cewa ta fara wasan da cin ƙwallaye biyu.

FSF ta ce an yanke shawarar kawo ƙarshen kwantaragin Pape Thiaw da ma’aikatansa ne a wani taron kwamitin zartarwa da aka gudanar ranar Asabar, inda aka yi nazari kan yadda ƙungiyar ta taka leda a gasar.

Hukumar ta kuma ɗora wa shugabanta, Abdoulaye Fall, alhakin sanar da kocin matakin a hukumance, tare da jagorantar sabon shirin sake fasalin manyan ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa na ƙasar.

Ana sa ran Abdoulaye Fall zai yi wa manema labarai bayani a Dakar ranar Litinin kan dalilan ɗaukar wannan mataki da kuma shirye-shiryen da hukumar ke yi domin farfaɗo da ƙwallon ƙafar Senegal.

Kafin fara Gasar Kofin Duniya ta 2026, an yi hasashen Senegal za ta kasance ɗaya daga cikin ƙasashen Afirka da za su iya taka rawar gani a fafutukar lashe kofin, sai dai ta kasa cika wannan fata bayan ficewarta daga gasar.