Senegal U-23: Gobe Najeriya za ta yi wasan karshe da Aljeriya
A gobe Asabar ne idan Allah Ya kai mu kungiyar kwallon kafa ta ’Yan kasa da shekara 23 (U-23) ta Najeriya za ta buga wasan karshe da takwararta ta kasar Aljeriya. Wasan zai gudana ne da misalin karfe takwas na dare agogon Najeriya. Kafin nan sai Senegal ta kece raini da Afirka ta Kudu a […]
A gobe Asabar ne idan Allah Ya kai mu kungiyar kwallon kafa ta ’Yan kasa da shekara 23 (U-23) ta Najeriya za ta buga wasan karshe da takwararta ta kasar Aljeriya. Wasan zai gudana ne da misalin karfe takwas na dare agogon Najeriya. Kafin nan sai Senegal ta kece raini da Afirka ta Kudu a wasan neman matsayi na uku da misalin karfe biyar na yamma agogon Najeriya.
Kafin Najeriya ta kai wannan matsayi, sai da ta doke Senegal mai masaukin baki a shekaranjiya Laraba da ci daya mai ban haushi ta hanyar bugun daga kai sai mai tsaron gida (fanariti). Haka kuma kafin a bayar da bugun fanaritin sai da alkalin wasa ya ba dan kwallon Senegal jan kati saboda rungumar kwallo da ya yi da hannunsa a cikin yadi na 18 a kokarinsa na hana kwallo ta fada ragarsu.
Cin da Najeriya ta yi wa Senegal dai shi ne na farko tun bayan da aka fara gasar, saboda ta samu nasara a wasanni ukun da ta yi ne a zagayen farko kafin haduwarta da Najeriya.
Yanzu dai Najeriya da Aljeriya sun haye zuwa gasar Olamfik da za a yi a Brazil a badi, tun da sun kai wasan karshe. Sannan kungiyar da ta zama ta uku a tsakanin Senegal da Afirka ta Kudu ita ma za ta haye gasar ta Olamfik din yayin da kasar da ta zama ta hudu kuma sai ta buga wasan gwajin-dafi (play-off) da wata kasa da Hukumar kwallon kafa ta Afirka (CAF) za ta sanar a nan gaba kafin ita ma haye gasar ta Olamfik.