Mun ba Tinubu sa’o’i 48 ya soke harajin tura kudi ta intanet —SERAP

Harajin ya saɓa wa kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 da kuma haƙƙin ɗan adam na ƙasa da ƙasa da alƙawuran da aka ɗauka.”

Mun ba Tinubu sa’o’i 48 ya soke harajin tura kudi ta intanet —SERAP

Ƙungiyar kare haƙƙin ’ƴan ƙasa da tabbatar da shugabanci na gari (SERAP) ta buƙaci shugaban ƙasa Bola Tinubu da ya umarci Babban Bankin Najeriya (CBN) ya janye harajin tura kudi ta intanet da ya ɗora wa ’yan kasar.

SEEAP ta ce harajin ya saɓa wa kundin tsarin mulkin Najeriya da kuma haƙƙin ɗan Adam na ƙasa da ƙasa.

SERAP ta kuma buƙaci Tinubu ya dakatar da ofishin mai ba shi shawara kan harkokin tsaro Nuhu Ribadu daga aiwatar da sabuwar dokar.

Ta buƙace shi da “ya umarci babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi, da ya gaggauta shiryawa tare da gabatar da ƙudirin gyara sashe na 44 da sauran tanade-tanaden dokar yaki da ta’addanci ta Intanet na 2024 ga Majalisar Dokoki ta ƙasa domin mayar da dokar daidai da kundin tsarin mulkin Najeriya da kuma haƙƙin ɗan Adam .”

A cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun mataimakin Daraktan SERAP, Kolawole Oluwadare, kungiyar ta ce: “Dole ne Gwamnatin Tinubu ta janye dokar a cikin sa’o’i 48 domin haramtacciyar dokar ta CBN.”

SERAP ta ce, “Sashe na 44(8) laifin rashin biyan harajin yanar gizo da ’yan Najeriya ke yi, haramun ne kuma ya saɓa wa tsarin mulki.”

Sanarwar ta ce: “Tuni lauyanmu Ebun-Olu Adegboruwa, SAN, ya fara shirya takardun da suka dace na kotu idan gwamnati ta gaza ko kuma ta yi watsi da shawararmu.

“Dole ne gwamnati ta gaggauta ɗaukar ƙwararan matakai don tabbatar da soke sashe na 44 da sauran tanade-tanaden dokar.

Fintiri ya ƙirƙiro sabbin masarautu 7 a Adamawa

Arewacin Najeriya bai dogaro da wani yanki ba – Ndume

Jagoran Syria ya sha alwashin kwance ɗamarar ƙungiyoyin da ke rike da makamai

Sojojin ruwa sun gina wa al’ummar Zariya asibiti kyauta