Serena Williams ta gina makarantu a kasashen Afirka uku
Shahararriyar ’yar kwallon Tennis ’yar kasar Amurka, Serena Williams ta gina makarantu a kasashen Afirka uku da suka hada da Uganda da Zimbabwe da Kenya da kuma wata a Jamaika da ke Amurka ta Kudu. ’Yar kwallon ta bayyana haka ne a shafin sadarwarta na Twitter a karshen makon jiya inda aka ga ta baza […]
Serena Williams
Shahararriyar ’yar kwallon Tennis ’yar kasar Amurka, Serena Williams ta gina makarantu a kasashen Afirka uku da suka hada da Uganda da Zimbabwe da Kenya da kuma wata a Jamaika da ke Amurka ta Kudu.
’Yar kwallon ta bayyana haka ne a shafin sadarwarta na Twitter a karshen makon jiya inda aka ga ta baza hotunan makarantun da ta gina a kasashen.
“Ina alfaharin shaida muku cewa na kammala gina makarantu ga marasa galihu a kasashen Uganda da Kenya da Zimbabwe da kuma Jamaika,” a wani rubutu da ta yi tare da hotunan.
Ta ce ta gina wadannan makarantu ne a kasashen Afirka don tallafa wa marasa galihu da ba su da ikon halartar makaranta. A cewarta wannan wani tallafi ne da take bayarwa ga mabukata a sassan duniya.
Williams ta gina wadannan makarantu ne a yankin Afirka a lokuta daban-daban tare da hadin gwiwar wata kungiya mai taimakon al’ummar Afirka mai suna Build Africa School inda ta gina makarantun a kasashen Uganda da Kenya da Zimbabwe.
Sannan ta hada gwiwa da wata kungiya mai suna Helping Hands Jamaica inda ta gina Makarantar Salt Marsh Elemantary School a Jamaika a kwana nan.
Serena ta ce tana gudanar da irin wannan taimako ne a kasashen da suka fi fuskantar talauci da kuma tashe-tashen hankula.
Tuni jama’a da dama musamman al’ummar da abin ya shafa suka aike da sakon fatan alheri ga Serena game da taimakon da ta yi musu.