…Sergio Ramos ya gargadi FC Barcelona

dan kwallon baya a kulob din Real Madrid Sergio Ramos ya gargadi kulob din FC Barcelona na Sifen a kan cewa ya daina yin tinkaho ganin yadda tauraruwarsa ke haskawa a halin yanzu inda ya ce komai zai iya faruwa a harkar kwallo.dan kwallon ya ce duk da yake kulob din Barcelona ne ya yi […]

…Sergio Ramos ya gargadi FC Barcelona
…Sergio Ramos ya gargadi FC Barcelona

dan kwallon baya a kulob din Real Madrid Sergio Ramos ya gargadi kulob din FC Barcelona na Sifen a kan cewa ya daina yin tinkaho ganin yadda tauraruwarsa ke haskawa a halin yanzu inda ya ce komai zai iya faruwa a harkar kwallo.
dan kwallon ya ce duk da yake kulob din Barcelona ne ya yi kaca-kaca da na Madrid a wasan El-Clasico kimanin makwanni biyu da suka wuce a gasar La-Liga da ci 4-0  akwai yiwuwar Madrid ta farfado kuma ta sake haye wa saman tebuin gasar kafin karshen kakar wasa ta bana.
“Ayanzu dai Barca ce take saman tebur, kuma ina yi musu murna, sai dai su sani komai na iya faruwa kamar yadda irin haka ta faru da mu a kakar wasan da ta wuce inda kafin karshen gasar reshe ya juye da mujiya, muka tashi a tutar babu bayan mun yi wasanni masu yawa ba tare da an doke mu ba”.
dan kwallon ya nanata cewa cin da Barcelona ta yi Madrid ya jefa ta cikin mawuyacin hali amma yanzu ta fara farfadowa bayan ta samu nasara a kan kulob din Eibar da ci 2-0 a ranar Lahadin da ta wuce.

Boko Haram sun ƙone makarantu a Borno

Har yanzu ’yan bindiga ba su saki matar Manjo Janar Rabe ba

An binne gawar Manjo Janar Rabe a Katsina

Wasu tsiraru ne ke rura matsalar tsaro a Najeriya — Christopher Musa