Sha uku-sha hudu
Wani mutum ne mai masifar karanbani,wata rana yana tafiya sai ya bi kusa da asibitin mahaukata. Abin mamaki sai ya ji muryar mahaukatan nan sun hada baki suna cewa: “Sha uku, sha uku,sha uku!” Sai ya je wurin ya leko su, domin ya ga wai mene ne sha uku? Sai ya leka wata kofa a […]
Wani mutum ne mai masifar karanbani,wata rana yana tafiya sai ya bi kusa da asibitin mahaukata. Abin mamaki sai ya ji muryar mahaukatan nan sun hada baki suna cewa: “Sha uku, sha uku,sha uku!” Sai ya je wurin ya leko su, domin ya ga wai mene ne sha uku? Sai ya leka wata kofa a katangar asibitin, inda wannan sauti ke fitowa. Da lekawarsa sai ya ji an soke masa ido daya da wani itace mai tsini. Take idonsa daya ya tsiyaye, yana dafe idon yana ihu sai ya ji mahaukatan sun dau tafi gaba dayansu raf-raf-raf, suna fadin: “Sha hudu, sha hudu, sha hudu!”
Daga Lawali Shehu Tsafe.