Sha Yabo: Muhammad (SAW)
Allah cikin ikonSa, muna cikin watan Rabi’ul Awwal, 1440 Bayan Hijira, watan da aka haifi fiyayyen talikai, Manzon Allah Muhammadu (saw). Mu nishadantu da wadannan baitoci goma sha daya daga alkalamin BASHIR YAHUZA MALUMFASHI (08065576011). Ya Allah Ka ba ni basira Rarraba mu da dukka asara Zan yabon mai hana tijara Sha yabo […]
Allah cikin ikonSa, muna cikin watan Rabi’ul Awwal, 1440 Bayan Hijira, watan da aka haifi fiyayyen talikai, Manzon Allah Muhammadu (saw). Mu nishadantu da wadannan baitoci goma sha daya daga alkalamin BASHIR YAHUZA MALUMFASHI (08065576011).
Ya Allah Ka ba ni basira
Rarraba mu da dukka asara
Zan yabon mai hana tijara
Sha yabo tuli ya sahara
Almustapha Daha Muhammad
*
Assalamu alaika Nabiyyu
Shugaban dukkan anbiya’u
Alhashimi Kuraishiyyu
Kai ne badadin Ya Alhayyu
Jinjina gare ka Muhammad
*
A halittu ba ka da tamka
Kyakkyawa ko ba wanka
Babban danni mai tanka
Girmanka ya wuce jinka
Sayyadi Rasulu Muhammad
*
Kai maliya ka wuce gulbi
Tsarki gare ka a kalbi
Aikinka gyaran kalbi
Tauraro ka wuce halbi
Baban Rukayya Muhammad
*
Dan Amina ka wuce daro
Ran Litinin kag gangaro
Ba kuka ba wani baro
Sai murmushi ka karo
Ya Aminu namu Muhammad
*
Na Khadijah babban gwarzo
Ga baituka naka murzo
Bisa izza duk na furzo
Makiyanka ni zan gurzo
Ya Habibu namu Muhammad
*
Ka fi ruwan sanyi a bazara
Kyauta wurinka ba tazara
Kyan daki sai da azara
Murmushi kullum ka zizara
Na A’isha jigo Muhammad
*
Ka fi zuma zaki ko madara
Kai kake izza ga mahara
Ja’irai sun zam a makara
Ba su da riba sai dai takura
Na Maimuna Maula Muhammad
*
A hakuri ka zarce dan damo
Ba ka murna da kankamo
Mai kaunarka ya kandamo
Alheri za ya fantamo
Maigidan Hafsat Muhammad
*
Ya Allah Ka kara baiwa
Da ni’ima wadda Kai wa
Ibrahim mai adawa
Da shirka ba ya halwa
Ga abban Zi Muhammad
*
Ya Allah Ka kara salati
Ga abban Nana Fati
Muna murna da party
Har ma mun rera baiti
Ga Daha guda Muhammad
***