Sha Yabo: Muhammadu (SAW)
A yau Jumu’a (12-08-1439) ta dace da zagayowar ranar haihuwar Manzon Allah, Muhammadu (saw). Dalili ke nan ya sanya Bashir Malumfashi (08065576011) ya tsara wadannan baitoci goma sha daya, domin yabo ga fiyayyen halitta: Ya Allah Ka ba ni basira, Rarraba mu da dukka asara, Zan yabon mai hana tijara, Sha yabo tuli ya […]
A yau Jumu’a (12-08-1439) ta dace da zagayowar ranar haihuwar Manzon Allah, Muhammadu (saw). Dalili ke nan ya sanya Bashir Malumfashi (08065576011) ya tsara wadannan baitoci goma sha daya, domin yabo ga fiyayyen halitta:
Ya Allah Ka ba ni basira,
Rarraba mu da dukka asara,
Zan yabon mai hana tijara,
Sha yabo tuli ya sahara,
Almustapha daha Muhammad.
Assalamu alaika Nabiyyu,
Shugaban dukkan anbiya’u,
Alhashimi kuraishiyyu,
Kai ne badadin Ya Alhayyu
Jinjina gare ka Muhammad.
A halittu ba ka da tamka,
Kyakkyawa ko ba wanka,
Babban danni mai tanka,
Girmanka ya wuce jinka,
Sayyadi Rasulu Muhammad.
Kai maliya ka wuce gulbi,
Tsarki gare ka a kalbi,
Aikinka gyaran kalbi,
Tauraro ka wuce halbi,
Baban Rukayya Muhammad.
dan Amina ka wuce daro,
Ran Litinin kag gangaro,
Ba kuka ba wani baro,
Sai murmushi ka karo,
Ya Aminu namu Muhammad.
Na Khadijah babban gwarzo,
Ga baituka naka murzo,
Bisa izza duk na furzo,
Makiyanka ni zan gurzo,
Ya Habibu namu Muhammad.
Ka fi ruwan sanyi a bazara,
Kyauta wurinka ba tazara,
Kyan daki sai da azara,
Murmushi kullum ka zizara,
Na A’isha jigo Muhammad.
Ka fi zuma zaki ko madara,
Kai kake izza ga mahara,
Ja’irai sun zam a makara,
Ba su da riba sai dai takura,
Na Maimuna Maula Muhammad.
A hakuri ka zarce dan damo,
Ba ka murna da kankamo,
Mai kaunarka ya kandamo,
Alheri za ya fantamo,
Maigidan Hafsat Muhammad.
Ya Allah Ka kara baiwa,
Da ni’ima wadda Kai wa,
Ibrahim mai adawa,
Da shirka ba ya halwa,
Ga abban Zi Muhammad.
Ya Allah Ka kara salati,
Ga abban Nana Fati,
Muna murna da party,
Har ma mun rera baiti,
Ga daha guda Muhammad.
—(SAW)—