Sha’aban: Da kintsa wa Ramadan (002)
Masallaci: Ba a fada ba Ibnu Rajab (RH) ya ce: “An ce kan azumin Sha’aban: azumtarsa kamar jarrabawar share fage ce ga azumin Ramadan, domin kada mutum ya shiga azumin Ramadan bisa wahala. Saboda yakan sa mutum ya san wani abu kan azumin tare da sabawa da shi, ya samu dandanon Ramadan ta hanyar azumin […]
Masallaci: Ba a fada ba
Ibnu Rajab (RH) ya ce: “An ce kan azumin Sha’aban: azumtarsa kamar jarrabawar share fage ce ga azumin Ramadan, domin kada mutum ya shiga azumin Ramadan bisa wahala. Saboda yakan sa mutum ya san wani abu kan azumin tare da sabawa da shi, ya samu dandanon Ramadan ta hanyar azumin Sha’aban, kuma ya shiga watan azumin Ramadan da karfin jiki da nishadi.”
Ya bayin Allah! Wanda azumin Sha’aban zai raunana shi daga yin azumin Ramadan, to ya dakatar da azumin idan Sha’aban ya je karshe, saboda fadinsa (SAW): “Idan Sha’aban ya kai karshe, kada ku yi azumi har zuwa Ramadan.” Ahmad da wasu suka ruwaito. Kuma Albani ya inganta shi, sai dai a isnadinsa akwai magana. Hanin da ke cikin wannan Hadisi domin a samu karfin yin azumin Ramadan ne. Wasu sun ce: “Hanin a kan wanda ya sha ruwa ne bai azumci farkon watan ba, don haka idan Sha’aban ya zama saura kadan ba zai yi azumi ba.
Na biyu: Ya kai bawan Allah da me za ka kintsa kanka domin Ramadan? Ka kintsa kanka da abin da ya sauwaka na ayyukan da’a, kamar yawaita karatun Alkur’ani da sadar da zumunta da sauran ayyukan kyautatawa. Salmata bin Kuhail ya ce: “Ya kasance ana cewa: “Watan Sha’aban watan masu karatu ne.” Abubakar Albalkhiy kuma ya ce: “Watan Rajab watan shuka, watan Sha’aban watan ban-ruwa ga shukar, watan Ramadan kuma watan girbe shukar ne. Wanda bai yi shuka a Rajab ba, bai bayar da ruwa ga shuka a Sha’aban ba, ta yaya zai yi girbi a Ramadan?”
Kuma ya ce: “Misalin Rajab kamar iska ce, misalin Sha’aban kuma kamar girgije ne, sannan misalin Ramadan kamar ruwan sama ne.”
Ya kai Musulmi! Rajab ya wuce me kake aikatawa a Sha’aban, idan kana nufin girbi a Ramadan? Ka dai ji halin Annabinka (SAW) da halin magabatan kwarai na wannan al’umma a cikin wannan wata, a wane matsayi kake game da wadannan ayyuka da darajoji? Ka yi sauri, ka yi gaggawa zuwa ga da’a ga Mabuwayi Mai yawan gafara.
Ina fadin wannan magana tawa ina neman gafarar Allah gare ni da ku, ku nemi gafararSa, lallai Shi Mai gafara ne Mai jinkai.
Huduba ta Biyu:
Godiya ta tabbata ga Allah bisa kyautatawarSa, muna yi maSa shukura a bisa dacewarSa da ni’imarSa. Na shaida ba wanda za a bauta maSa da gaskiya sai Allah Shi kadai girmamawa ga sha’aninSa. Kuma ina shaidawa lallai Annabi Muhammad bawanSa ne kuma ManzonSa ne, mai kira zuwa ga yardarSa. Allah Ya kara tsira da aminci a gare shi da alayensa da sahabbansa da ’yan uwansa.
Bayan haka, ku sani-ya bayin Allah!- Lallai akwai shiriya da haske a cikin Littafin Allah da Sunnar AnnabinSa (SAW). bata da kuma rudu suna cikin abin da yake sabaninsu; “To wanda ya bi shiryarwaTa, ba ya bacewa, kuma ba ya wahala. Kuma wanda ya bijire daga ambatoNa, (Alkur’ani), to, lallai ne rayuwa mai kunci ta tabbata a gare shi, kuma Muna tayar da shi a Ranar kiyama yana makaho.” (k: 20: 23-24).
Bayin Allah! Daga cikin manyan abubuwan da mutum zai tarbi Ramadan da su a watan Sha’aban akwai abin da dabarani da Ibnu Hibban suka ruwaito daga Mu’azu bin Jabal (RA) daga Annabi (SAW) ya ce: “Allah Yana duban daukacin bayinSa a daren rabin Sha’aban, sai ya gafarta wa dukkan bayinsa, face mushiriki da muhashin.”
Don haka ku tsare tauhidinku, ya ku bayin Allah! Kada ku yarda babba ko karamar shirka su warware shi. Ku tsarkake kawunanku daga rowa da keta da bakin rai da kuncin zuciya. Domin Allah Madaukaki Yana gafartawa a daren rabin Sha’aban ga dukkan bayinsa face mushiriki da muhashin. Kashedinku da yi wa Allah shirki, mu binciki kawunanmu, domin ta yiwu dayanmu an jarrabe shi da wani abu daga shirki amma bai sani ba. Mushiriki shi ne wanda ya bauta wa wanin Allah da kowane nau’i na ibada. Wanda ya kirayi wanin Allah ko ya yi bakace da shi, ko ya yi yanka dominsa ko makamancin haka na daga ayyukan ibada, hakika ya yi shirka, kuma ya cancanci ukuba, ita ce rashin samun gafara da tabbata a wuta. Allah Ya ce: “Lallai shi wanda ya yi wa Allah shirki, hakika Allah Ya haramta masa Aljanna kuma makomarsa wuta ce, azzalumai ba su da wani mataimaki.” (k5:72). Kuma Allah Ya ce: “Lallai Allah ba Ya gafartawa a yi shirki da Shi, amma Yana gafarta abin da bai kai haka ba, ga wanda Ya so. Wanda ya yi shirki da Allah, hakika ya bace, bacewa mai nisa.” (k:4:116).
Muhashin shi ne mai gaba ko mai husuma ko mai yanke zumunta ko mai juya baya a fagen jihadi ko mai hasada ko mai kullatar mutane a zucci. Dukkan wadannan siffofi ne na muhashin. Kuma suna jawo rashin samun gafara.
An karbo daga Abu Huraira (Allah Ya kara masa yarda) a Hadisi Marfu’i cewa: “Ana bude kofofin Aljanna a ranakun Litinin da Alhamis, sai a gafarta wa kowane bawa da ba ya shirki da Allah, face wanda ya kullaci dan uwansa. Sai Ya ce: “Ku dubi wadannan biyu har sai sun sulhunta.” Muslim ya ruwaito. Daga Abu Sa’alabata Al-Khushni daga Annabi (SAW) ya ce: “Lallai Allah Yakan duba bayinSa a daren rabin Sha’aban, sai Ya gafarta wa muminai, Ya yi wa kafirai talala, sannan Ya kyale masu hasada da kullatar juna da hasadarsu ko kullatarsu, har sai sun bari.” dabarani ya ruwaito, kuma shi ne Hadisi na 1144 a Silsilatus Sahiha. kullin da ake nufi shi ne yanke zumunta da bata tsakanin mutane.
Annabi (SAW) ya ce: “Wata cuta ta al’ummar da ta gabace ku, za ta shigo cikinku: Hasada da gaba. Ita mai askewa ce. Ban ce tana aske gashi ba, a’a tana aske addini. Na rantse da wanda raina ke hannunSa, ba za ku shiga Aljanna ba har sai kun yi imani, kuma ba za ku yi imani ba, har sai kun so juna. Ko kuna son in nuna muku abin da zai sa ku so juna? Ku yawaita yin sallama (ko zaman lafiya) a tsakaninku.”
Don haka hada shirka da kullata na nuni da cewa dukkansu suna aske addini su bata shi. Bambanci kawai shi ne shirka na bata addini ba ta barin komai daga gare shi, yayin da gaba da hasada da yanke zumunta da sauransu suke fatattaka shi su bar shi ba ya da ruhi, koda ba su tuttuge shi daga tushe ba. kullata da hasada suna bata addini suna aske shi. Hasada da keta da kullata ba su shiga zukata face sun zama sababi na raunin imani, kuma suna iya raba mutum da imani baki daya, kamar yadda ya faru da Iblis lokacin da ya yi hasada ya kullaci Annabi Adam (AS). Don haka Allah Ya yi gargadi mai karfi kansu, Ya ambace su tare da zunubi mafi girma wato shirka. Domin shirka tana bata alakar mutum da Ubangijinsa, yayin da kullata da hasada ke bata alakarsa da ’yan uwansa muminai. Idan alakar mutum ta baci a tsakaninsa da Ubangijinsa da kuma muminai, shi ke nan babu abin da ya saura a addininsa. Ta yaya Allah zai gafarta masa?! Don haka ne aka haramta masa falalar wancan dare mai albarka.
Ku saurara! Wadansu mutane sukan kebance ranar dare rabin Sha’aban da azumi da tsayuwar dare da wasu nau’o’in addu’o’i da zikirori da rera wakoki. To dukkan wadannan ba su tabbata ba daga Hadisin Annabi (SAW). Iyaka an samu hakan ne ko a Hadisi mai rauni ko kirkirarre da aka yi wa Annabi (SAW) karya, kamar yadda Ibnu Rajab da wadansu suka ce. Dukkan wadannan (Hadisai) ba a kafa hujja da su, kuma ba a aiki da su a hukunce-hukunce.
Amma duk mutumin da ya saba tsayuwar dare, to, ba zai bar tsayuwar daren a wannan ranar ba. Kuma duk wanda ya saba yin azumin nafila, idan ya dace da daren rabin Sha’aban, sai ya yi azuminsa ba zai bari ba. Haka ma wanda ya saba azumi a Sha’aban ya azumce shi (ranar rabin Sha’aban) yana mai koyi da Annabi (SAW). Ku tafi a kan shiriyar Annabinku (SAW) wadda take sadarwa zuwa ga Aljanna. Ku kiyayi hanyoyin bata da bidi’a, masu sadarwa zuwa ga gidan halaka.