Sha’aban: Da kintsa wa Ramadan 01
Masallaci: Ba a fada ba Huduba ta farkoGodiya da taslimi:Bayan haka, ya ku bayin Allah! Lallai mumini zai rika ganin juyi a wannan zamani idan Allah Ya tsawaita rayuwarsa. A kowace rana zai rika samun ganimar da zai yi guzurin Lahira da ita. Allah Madaukaki Ya ce: “Kuma Shi ne Wanda Ya sanya dare da […]
Masallaci: Ba a fada ba
Huduba ta farko
Godiya da taslimi:
Bayan haka, ya ku bayin Allah! Lallai mumini zai rika ganin juyi a wannan zamani idan Allah Ya tsawaita rayuwarsa. A kowace rana zai rika samun ganimar da zai yi guzurin Lahira da ita. Allah Madaukaki Ya ce: “Kuma Shi ne Wanda Ya sanya dare da yini a kan mayewa, ga wanda yake son ya yi tunani, ko kuwa ya yi nufin ya gode.” (k: 25:62).
Ya ku muminai! Mun shigo watan Sha’aban, mai rabo ya samu rabo a watan Rajab, ta wajen ayyukan da’a da kusanci ga Allah. To ga shi mun shigo watan Sha’aban me muka shirya aikatawa a cikinsa? Wannan huduba kan wannan wata za ta nazarci darussa da wasu abubuwa da suka shafi falala da hukunce-hukuncensa. Za mu nazarci rayuwar Manzonmu (SAW) a cikinsa domin yin koyi da shi. Me ya zo mana dangane da falalarsa? Me ya zo a cikinsa na hukunce-hukuncensa? Me Annabi (SAW) yake yi idan watan Sha’aban ya shigo?
An kira shi da watan Sha’aban ne saboda Larabawa suna watsuwa a cikinsa domin neman ruwa. Wasu sun ce, ana kiransa haka ne saboda watsuwarsu wajen kai hare-haren yaki bayan fita daga watan Rajab Mai alfarma. Wasu kuma suka ce an kira shi da haka ne saboda wata ne da ke bayyana a tsakanin Rajab da Ramadan.
Amma falalarsa da abin da ake so a rika yi a cikinsa, hakika ya zo daga Ahmad da wasu, kuma Ibnu Khuzaima ya inganta shi, sannan Albani ya kyautata shi daga Usama bin Zaid, ya ce: “Na ce: “Ya Manzon Allah! Ban gan ka kana azumtar wani wata kamar yadda kake azumtar Sha’aban ba! Sai ya ce: “Wannan wata ne da mutane suke gafala daga gare shi a tsakanin Rajab da Ramadan. Shi ne watan da ake daukaka ayyuka zuwa ga Ubangijin talikai. Don haka nake son a daukaka aikina ina cikin azumi.”
Ya ku Musulmi! Ba ku ganin yadda mutane suke gafala a yau daga watan Sha’aban? Suna gafala daga ayyukan da’a da neman kusanci ga Allah. Suna nutso a cikin sha’awoyi da ayyukan jin dadi. Suna gafala daga Sha’aban alhali Manzon Allah (SAW) ya kasance yana raya shi da ayyukan da’a da azumi, ya ce da Usama: “Wannan wata ne da mutane suke gafala daga gare shi a tsakanin Rajab da Ramadan.”
Mutane suna gafala ne daga Sha’aban saboda yana tsakanin watanni biyu masu girma wato Rajab Mai alfarma da Ramadan Mai albarka. Mutane sun fi shagala da su biyun don haka sai aka shagaltar da su daga Sha’aban. Ta kai wasu mutane suna ganin azumin watan Rajab (azumin tsofi inji Hausawa), ya fi azumin Sha’aban, saboda shi Rajab wata ne Mai alfarma. Wannan ba daidai ba ne, azumin Sha’aban ya fi na Rajab falala saboda fadin Annabi (SAW): “Ana daukaka ayyuka a cikinsa, kuma ina son a daukaka aikina ina azumi.”
Hakika malamai (Rahimahumullahu) sun ce: “A cikin wannan Hadisi akwai dalili cewa mustahabbi ne a raya lokutan da mutane suka gafala daga ayyukan da’a, kuma hakan abin so ne a wurin Allah Mabuwayi.”
Don haka ku koma ga Allah ya ku bayin Allah! Ku sallama ga abin da Yake yarda da shi, domin lada da ijara suna kara martaba idan aka yi su a lokacin da mutane suka gafala, fa’idojin raya shi da da’a ita ce mafi girma. Kuma wadannan fa’idoji za a same su ne idan aka yi ayyukan da’ar a asirce. Sirrantan aikin da’a daya ne daga cikin manya sabubban karbar aiki. Akwai bukatar aiki ya kasance don Allah, a nesanta shi daga jiyarwa da riya.
Ku sani aikin da’a a lokacin gafalar mutane yana da wahala a tsakanin mutane. Kuma mafiya falalan ayyuka, su ne wadanda suka fi wahala ga mutane matukar sun dace da Sunnar Annabi (SAW). Manzon Allah (SAW) yana cewa: “Ladar aiki ya dogara ne da irin wahalar da aka sha.”
Ya bayin Allah! Lallai ana daukaka ayyukan shekara zuwa ga Allah Madaukaki a watan Sha’aban. Ayyukan bayi suna bijirowa ga Allah bijirowa a kowane yini da dare, sannan ayyukan mako su bijiro gare shi a kowace Litinin da Alhamis, sannan a bijiro da ayyukan shekara a Sha’aban. Ga kowace bijirowa akwai hikima, Allah Yana bayyana su ga wanda Ya so daga cikin halittunsa, ko Ya asirta shi a wurinSa, tare da cewa babu abin da Yake boyuwa ga Allah Madaukaki daga ayyukan bayinSa.
Ya ku muminai, a yayin da Sha’aban ya zama kamar zagi ga watan Ramadan-kuma ba makawa ga tattalin bakon da ke zuwa- sai aka shari’anta yin azumi da sauran ayyukan da’a a cikinsa domin kusantar Allah ta yadda za a yi tattalin zuwan Ramadan, a tare shi cikin annashuwa da shauki da sabo wajen da’a ga Mai rahama. Don haka ne Annabi (SAW) yake yawaita azumi a cikinsa, yake cin ganimar lokacin gafalar mutane duk da matsayinsa, shi ne Manzon Allah (SAW), shi ne wanda aka gafarta masa abin da ya gabatar da wanda ya jinkintar na zunubinsa. Don haka magabatan kwarai suke kara kokari a Sha’aban suke tattalin zuwan Ramadan.
Ya kai bawan Allah! Me ka kintsa a cikin wannan wata na Sha’aban don tarbar Ramadan? Wane tattali ka yi masa? Saurara Allah Ya tsare ka; na farko ka yi tattalin ranka cikin abin da Manzon Allah (SAW) ya kwadaitar maka, wato yawaita azumi a wannan wata. Hakika (SAW) ya kasance yana yawaita azumi a cikinsa. An karbo daga A’isha (RA) ta ce: “Manzon Allah (SAW) ya kasance yana azumi har sai mun ce ba ya shan ruwa, kuma yana shan ruwa har sai mun ce ba ya azumi. Amma ban taba ganin Manzon Allah (SAW) ya yi azumin wata guda ba, sai Ramadan. Kuma ban taba ganinsa ya yawaita azumi a wani wata fiye da Sha’aban ba.” Buhari da Muslim suka ruwaito.
A wata ruwaya ta Buhari ya ce, “Ya kasance yana azumtar Sha’aban dukkansa.” Muslim kuma ya ruwaito cewa: “Yana azumtar Sha’aban sai dan kadan.” A ruwayar Abu Dawud ta ce: “Watan da Manzon Allah (SAW) ya fi son ya azumta shi ne Sha’aban, sannan ya sadar da shi da Ramadan.”
Dukkan wadannan Hadisai ingantattu ne, kuma wannan yana nuni ne da tsananin kiyayewarsa ga yin azumi a cikin Sha’aban. Kuma manufa ita ce ya fi yin azumi a cikinsa, ba wai yana azumtarsa gaba daya ba.
Ibnu Hajrin (RH) ya ce: “Ya fi yin azumin tadawwa’i a cikin Sha’aban fiye da kowane wata. Ya kasance yana azumtar mafi yawan kwanakin Sha’aban.”
Ya ku Musulmi! Malamai sun ce: “Yin azumi a Sha’aban ya fi falala daga yin azumi a sauran watanni kamar azumin Muharram, wanda shi ne mafi falalar azumi a bayan Ramadan. Domin falalar azumin tadawwa’i, shi ne ya kasance a kusa da azumin farilla na Ramadan a gabansa ko bayansa. Idan yana daf da azumin Ramadan sai ya zamo kamar an jeranta azumin sunnoni da na farilla a gabansa ko bayansa. Don haka azumin Sha’aban kamar Sunnah ce ta kabliyya ga Ramadan, yayin da azumin shida na Shawwal suke zaman ba’adiyya ga Ramadan. Don haka jerantattun sunnoni sun fi tadawwa’in da ke zaman kansa cikin abin da ya shafi Sallah. To kamar haka lamarin yake, cewa yin azumi a gabani ko bayan Ramadan ya fi falala daga yin azumin da bai saduwa da shi.