Sha’aban da kintsa wa Ramadan (2)
Yaseen Bi’asba’i Masallaci: Ba a fada ba Fassarar Salihu Makera Ya kai Musulmi! Rajab ya wuce, me kake yi a Sha’aban, idan kana nufin girbi a Ramadan? Ka dai ji halin Annabinka (SAW) da magabatan kwarai na wannan al’umma a cikin wannan wata, a wane matsayi kake kan wadannan ayyuka da darajoji? Ka yi gaggawa […]
Yaseen Bi’asba’i
Masallaci: Ba a fada ba
Fassarar Salihu Makera
Ya kai Musulmi! Rajab ya wuce, me kake yi a Sha’aban, idan kana nufin girbi a Ramadan? Ka dai ji halin Annabinka (SAW) da magabatan kwarai na wannan al’umma a cikin wannan wata, a wane matsayi kake kan wadannan ayyuka da darajoji? Ka yi gaggawa zuwa ga da’a ga Mabuwayi Mai yawan gafara.
Huduba ta Biyu
Godiya ta tabbata ga Allah a bisa kyautatawarSa, muna yi maSa shukura a bisa dacewa da ni’imarSa. Na shaida ba wanda za a bauta maSa da gaskiya sai Allah Shi kadai, girmamawa ga sha’aninSa. Kuma na shaida lallai Annabi Muhammad bawanSa ne kuma ManzonSa ne, mai kira zuwa ga yardarSa. Allah Ya kara tsira da aminci a gare shi da alayensa da sahabbansa da ’yan uwansa.
Bayan haka, ku sani-ya bayin Allah!- Lallai akwai shiriya da haske a cikin Littafin Allah da Sunnar AnnabinSa (SAW). Bata da rudu suna cikin abin da yake sabaninsu; “To wanda ya bi shiryarwaTa, to, ba ya bacewa, kuma ba ya wahala. Kuma wanda ya bijire daga ambatoNa (Alkur’ani), to, lallai ne rayuwa mai kunci ta tabbata a gare shi, kuma Muna tayar da shi a Ranar Kiyama yana makaho.” (K:20: 23-24).
Bayin Allah! Daga cikin manyan abubuwan da mutum zai taryi Ramadan da su a watan Sha’aban akwai abin da Dabarani da Ibn Hibban suka ruwaito daga Mu’azu bn Jabal (RA) daga Annabi (SAW) ya ce: “Allah Yana duban daukacin bayinSa a Daren Rabin Sha’aban, sai ya gafarta wa dukkan bayinsa, face mushiriki da muhashin.”
Don haka ku tsare tauhidinku, ya ku bayi Allah! Kada ku yarda babba ko karamar shirka su warware shi. Ku tsarkake kawunanku daga rowa da keta da bakin rai da kuncin zuciya. Domin Allah Madaukaki Yana gafartawa a Daren Rabin Sha’aban ga dukkan bayinSa face mushiriki da muhashin. Kashedinku da yi wa Allah shirki, mu binciki kawunanmu, domin ta yiwu dayanmu an jarrabe shi da wani abu daga shirki amma bai sani ba. Mushiriki shi ne wanda ya bauta wa wanin Allah da kowane nau’i na ibada. Wanda ya kirayi wanin Allah ko ya yi bakace da shi, ko ya yi yanka dominsa ko makamancin haka na daga ayyukan ibada, hakika ya yi shirka, kuma ya cancanci ukuba, ita ce rashin samun gafara da tabbata a wuta. Allah Ya ce: “Lallai ne shi wanda ya yi wa Allah shirki, hakika Allah Ya haramta masa Aljanna kuma makomarsa wuta ce, azzalumai ba su da wani mataimaki.” (K5:72). Kuma Allah Ya ce: “Lallai Allah ba Ya gafartawa a yi shirki da Shi, amma Yana gafarta abin da bai kai haka ba, ga wanda Ya so. Wanda ya yi shirki da Allah, hakika ya bace bacewa mai nisa.” (K:4:116).
Muhashin shi ne mai gaba ko mai husuma ko mai yanke zumunta ko mai juya baya a fagen jihadi ko mai hassada ko mai kullatar mutane a zuci. Dukkan wadannan siffofi ne na muhashin. Kuma suna jawo rashin samun gafara.
An karbo daga Abu Huraira (Allah Ya kara masa yarda) marfu’i cewa: “Ana bude kofofin Aljanna a ranakun Litinin da Alhamis, sai a gafarta wa kowane bawa da ba ya shirki da Allah, face wanda ya kullaci dan uwansa. Sai Ya ce: “Ku dubi wadannan biyu har sai sun sulhunta.” Muslim ya ruwaito. Daga Abu Sa’alabatu Alkhushni daga Annabi (SAW) ya ce: “Lallai Allah Yakan duba bayinSa a Daren Rabin Sha’aban, sai Ya gafarta wa muminai, Ya yi wa kafirai talala, sannan Ya kyale masu hassada da kullatar juna da hassadarsu ko kullatarsu, har sai sun bari.” Dabarani ya ruwaito, kuma shi ne Hadisi na 1144 a Silsilatus Sahiha.
Kullin da ake nufi shi ne yanke zumunta da bata tsakanin mutane.
Annabi (SAW) ya ce: “Wata cuta ta al’ummar da ta gabace ku, za ta shigo cikinku: Hassada da gaba. Ita mai askewa ce. Ban ce tana aske gashi ba, a’a tana aske addini. Na rantse da wanda raina ke hannunSa, ba za ku shiga Aljanna ba har sai kun yi imani, kuma ba za ku yi imani ba, har sai kun so juna. Ko kuna son in nuna muku abin da zai sa ku so juna? Ku yawaita yin sallama (ku watsa zaman lafiya) a tsakaninku.”
Don haka hada shirka da kullata na nuni da cewa dukkansu suna aske addini su bata shi. Bambanci kawai shi ne shirka na bata addini ba ta barin komai daga gare shi, yayin da gaba da hassada da yanke zumunta da sauransu suke fatattaka shi su bar shi ba ya da ruhi, koda ba su tuttuge shi daga tushe ba. Kullata da hassada suna bata addini suna aske shi. Hassada da keta da kullata ba su shiga zukata face sun zama sababi na raunin imani, kuma suna iya raba mutum da imani baki daya, kamar yadda ya faru da Iblis lokacin da ya yi hassada ya kullaci Annabi Adam (AS). Don haka Allah Ya yi gargadi mai karfi a kansu, Ya ambace su tare da zunubi mafi girma wato shirka. Domin shirka tana bata alakar mutum da Ubangijinsa, yayin da kullata da hassada suke bata alakar mutum da ’yan uwansa muminai. Idan alakar mutum ta baci a tsakaninsa da Ubangijinsa da kuma muminai, shi ke nan babu abin da ya saura a addininsa. Ta yaya Allah zai gafarta masa? Don haka ne aka haramta masa falalar wancan dare mal albarka.
Ku saurara! Wadansu mutane sukan kebance ranar Daren Rabin Sha’aban da azumi da tsayuwar dare da wasu nau’o’in addu’o’i da zikirori da rera wakoki. To dukkan wadannan ba su tabbata daga Annabi (SAW) ba. Iyaka an samu hakan ne ko a Hadisi mai rauni ko kirkirarre da aka yi wa Annabi (SAW) karya, kamar yadda Ibn Rajab da wadansu suka ce. Dukkan wadannan (hadisai) ba a kafa hujja da su, kuma ba a aiki da su a hukunce-hukunce.
Amma duk mutumin da ya saba tsayuwar dare, to, ba zai bar tsayuwar daren a wannan ranar ba. Kuma duk wanda ya saba yin azumin nafila, idan ya dace da Daren Rabin Sha’aban, sai ya yi azuminsa ba zai bari ba. Haka ma wanda ya saba azumi a Sha’aban ya azumce shi (Ranar Rabin Sha’aban) yana mai koyi da Annabi (SAW). Ku tafi a kan shiriyar Annabinku (SAW) wadda take sadarwa zuwa ga Aljanna. Ku kiyayi hanyoyin bata da bidi’a, masu sadarwa zuwa ga gidan hallaka.
Ya ku masu biyayya da zababbu! Ku fuskanci wannan wata da tuba na gaskiya daga shirki da bidi’a, ku fuskance shi da istigfari.
Ramadan ya darkako, saura kadan ya kankama, don haka ya kai Musulmi! Me ka tanada ga Ramadan? Da me ka kintsa kanka?
Hakika wadansu mutane da ’ya’yansu sun mutu. Wadansu mutane sun rabauta, wadansu kuma sun tabe. Wadansu sun shiryu, wadansu sun bace. Don haka ka auna ni’imar Allah a kanka, ka roke Shi Ya kai ka Ramadan, ka kara himma a al’amuranka.
Ya kai mai zunubi! Ka koma ga Ubangijinka! Ya kai mai gujewa da kauracewa ko wulakanta iyaye! Ka koma ga kyautata musu! Ya kai mai yanke zumunta da rashin kyautata wa makwabta ka koma ga sadar da zumunta da kyautata wa makwabta!
Sha’aban yana kiranka, yana nemanka, ka zo ka tsarkake kanka, ka sabunta zuciyarka, ka wanke kurar rarraba kai da bin son zuciya da rike wasi-wasin Shaidan. Ka yi kwadayin abin da zai amfane ka, ka yi kusan barin duniya, kuma ka yi kusan isa Lahira!
Lallai Allah Ya yi muku umurni da wani al’amari da Ya fara da kanSa, Ya yabi Mala’iku masu tasbihi game da tsarkake Shi a kansa, Ya fadi magana wadda take mai girma: “Lallai Allah da Mala’ikunSa suna salati ga Annabi, ya ku wadada suka yi imani! Ku yi salati a gare shi, kuma ku yi taslimi tare da sallamawa.” (K:33:56)
Don haka ku yi salati da taslimi a bisa mafi tsarkin mutane. Allahumma salli wa sallim ala Abdika wa Rasulika Muhammad, wa’ardi Allahumma an khulafa’ihil abrar wa sahabatihil adhar, almuhajirina minhum wal’ansar, wa’anna ma’ahum bi-judika wa-afwika Ya Azizu Ya Gaffar!
Allahumma a’izzal Islama wa Musulimin, wa dammir dughata walmu’utadin, wan shiril amni wa istikrari warrakha’i fi jami’i biladil Muslimina Ya Rabbil alamin.