Sha’aban: Da kintsa wa Ramadan

Watan da Manzon Allah (SAW) ya fi son ya azumta shi ne Sha’aban.

Sha’aban: Da kintsa wa Ramadan

Masallaci

Dukkan Yabo da Godiya sun tabbata ga Allah Ubangijin Talikai. 

Bayan haka, ya ku bayin Allah! Lallai mumini zai rika ganin juyi a wannan zamani idan Allah Ya tsawaita rayuwarsa, ta yadda a kowace rana zai rika samun ganimar da zai yi guzurin Lahira da ita.

Allah Madaukaki Ya ce: “Kuma Shi ne Wanda Ya sanya dare da yini a kan mayewa, ga wanda yake son ya yi tunani ko kuwa ya yi nufin ya gode.” (K: 25:62).

Ya ku muminai! Mai rabo, ya sami rabo a watan Rajab, ta wajen ayyukan da’a da kusanci ga Allah. To ga shi mun shigo watan Sha’aban, me muka shirya yi a cikinsa?

An kira wannan wata Sha’aban ne saboda Larabawa suna watsuwa a cikinsa don neman ruwa.

Wadansu kuma sun ce, ana kiransa da haka ne saboda watsuwarsu wajen kai hare-haren yaki bayan fita daga watan Rajab Mai alfarma.

Amma wadansu sun ce saboda wata ne da ke bayyana, a tsakanin Rajab da Ramadan.

Dangane da falalarsa da abin da ake son a yi a cikinsa, hakika ya zo daga Ahmad da wadansu, kuma Ibn Khuzaima ya inganta shi, sannan Albani ya kyautata shi daga Usama bn Zaid.

Ya ce: “Na ce: “Ya Manzon Allah! Ban gan ka kana azumtar wani wata kamar yadda kake azumtar Sha’aban ba!

Sai ya ce: “Wannan wata ne da mutane suke gafala daga gare shi a tsakanin Rajab da Sha’aban.

“Shi ne watan da ake daukaka ayyuka zuwa ga Ubangijin talikai. Don haka nake son a daukaka aikina ina cikin azumi.”

Ya ku Musulmi! Ba ku ganin yadda mutane suke gafala daga watan Sha’aban?

Suna gafala daga ayyukan da’a da kusanta ga Allah. Suna nutso a cikin sha’awoyi da ayyukan jin dadi.

Suna gafala daga Sha’aban alhali Manzon Allah (SAW) ya kasance yana raya shi da ayyukan da’a da azumi.

Ku tuna ya ce wa Usama: “Wannan wata ne da mutane suke gafala daga gare shi a tsakanin Rajab da Ramadan.”

Mutane suna gafala daga Sha’aban saboda yana tsakanin watanni biyu masu girma wato Rajab da Ramadan.

Mutane sun fi shagala da watanni biyun, don haka sai aka shagaltar da su daga gare shi.

Ta kai wadansu mutane suna ganin azumin watan Rajab (azumin tsofi in ji Hausawa), ya fi azumin Sha’aban, saboda shi Rajab wata ne Mai alfarma.

Wannan ba daidai ba ne, azumin Sha’aban ya fi na Rajab falala saboda fadin Annabi (SAW): “Ana daukaka ayyukan a cikinsa, kuma ina son a daukaka aikina ina azumi.”

Hakika malamai (Allah Ya yi musu rahama) sun ce: “A cikin wannan Hadisi akwai dalili cewa mustahabbi ne a raya lokutan da mutane suka gafala da ayyukan da’a, kuma hakan abin so ne a wurin Allah Mabuwayi.”

Don haka ku koma ga Allah ya ku bayin Allah! Ku sallama ga abin da Yake yarda da shi, domin lada da ijara suna kara martaba idan aka yi su a lokacin da mutane suka gafala, fa’idojin raya shi da da’a ita ce mafi girma.

Kuma waɗannan fa’idoji za a same su ne idan aka yi ayyukan da’ar a asirce tare da boyewa.

Sirrantawa da aikata aikin da’a a boye daya ne daga cikin manya sabubban karbar aiki.

Akwai bukatar aiki ya kasance don Allah, a nesanta shi daga jiyarwa da riya.

Ku sani aikin da’a a lokacin gafalar mutane yana da wahala a tsakanin mutane.

Mafi falalar ayyuka, shi ne wanda ya fi wahala ga mutane matukar ya dace da Sunnar Annabi (SAW) Manzon Allah (SAW) ya ce: “Ladar aiki na dogara ne da irin wahalar da aka sha.”

Ya bayin Allah! Lallai ana daukaka ayyukan shekara zuwa ga Allah a watan Sha’aban.

Ayyukan bayi suna bijirowa ga Allah bijirowa a kowane wuni da dare, sannan ayyukan mako su bijiro gare Shi a kowace Litinin da Alhamis, sannan a bijiro da ayyukan shekara a Sha’aban.

Ga kowace bijirowa akwai hikima, Allah Yana bayyana su ga wanda Ya so daga cikin halittunSa, ko Ya asirta shi a wurinSa, alhali babu abin da Yake boyuwa ga Allah daga ayyukan bayinSa.

Ya ku muminai! A yayin da Sha’aban ya zama kamar kofar shiga Ramadan-kuma ba makawa ga tattalin zuwansa- sai aka shar’anta yin azumi da sauran ayyukan da’a a cikin Sha’aban domin kusantar Allah ta yadda za a yi tattalin zuwan Ramadan, a tarbe shi cikin annashuwa da shauki da sabawa da da’a ga Mai rahama.

Don haka ne Annabi (SAW) yake yawaita azumi a cikinsa, yake cin ganimar lokacin gafalar mutane duk da matsayinsa, na wanda aka gafarta masa abin da ya gabatar da wanda ya jinkintar na zunubinsa.

Don haka ne magabatan kwarai suke kara kokari a Sha’aban suke tattalin zuwan Ramadan.

Ya kai bawan Allah! Me ka shirya a Sha’aban don marabtar Ramadan? Wane tattali ka yi masa?

Ka yi tattalin kanka da abin da Manzon Allah (SAW) ya kwadaitar, wato yawaita azumi a watan. Hakika Annabi (SAW) yana yawaita azumi a cikinsa.

An karbo daga A’isha (Allah Ya yarda da ita da mahaifinta) ta ce: “Manzon Allah ya kasance yana azumi har sai mun ce ba ya sha ruwa, kuma yana shan ruwa har sai mun ce ba ya azumi.

“Amma ban taba ganin Manzon Allah (SAW) ya yi azumin wata guda ba, sai Ramadan. Kuma ban taba ganin ya yawaita azumi a wani wata fiye da Sha’aban ba.” Buhari da Muslim suka ruwaito.

A wata ruwaya ta Buhari ya ce, “Ya kasance yana azumtar Sha’aban dukkansa.” Muslim kuma ya ruwaito cewa: “Yana azumtar Sha’aban sai dan kadan.”

A ruwayar Abu Dawud ta ce: “Watan da Manzon Allah (SAW) ya fi son ya azumta shi ne Sha’aban, sannan ya sadar da shi da Ramadan.”

Dukkan wadannan Hadisai ingantattu ne, kuma wannan yana nuni ne da tsananin kiyayewarsa ga azumi a cikin Sha’aban.

Manufa ita ce ya fi yin azumi a cikinsa ba wai yana azumtarsa gaba daya ba.

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos

Kasuwar Laranto da ke Jos ta yi gobara

Ɗan shekara 60 ya rasu bayan faɗawa a rijiya a Kano