Sha’awar aikin jarida ya hana ni zama lauya – Ibrahim Alfa
Malam Ibrahim Alfa Ahmed na gidan Rediyon Muryar Amurka na daya daga cikin fitattun ma’aikatan gidan rediyo da miliyoyin jama’a ke sauraro a sassan duniya. Ya bulle da shirye-shirye da suka hada da fitaccen shirin nan nasa na ‘A bari ya huce…’ A tattaunawarsu da wakilinmu ya ce sha’awar aikin jarida ne ya sanya ya […]
Malam Ibrahim Alfa Ahmed na gidan Rediyon Muryar Amurka na daya daga cikin fitattun ma’aikatan gidan rediyo da miliyoyin jama’a ke sauraro a sassan duniya. Ya bulle da shirye-shirye da suka hada da fitaccen shirin nan nasa na ‘A bari ya huce…’ A tattaunawarsu da wakilinmu ya ce sha’awar aikin jarida ne ya sanya ya yi watsi da karatun aikin lauya:
Aminiya: Wane ne Ibrahim Alfa Ahmed?
Ibrahim Alfa: Ni mutumen Bauchi ne a Arewacin Najeriya, na yi makarantar firamare a garin Bauchi, na yi sakandare a garin Potiskum da ke Jihar Yobe, wato (GSS Potiskum) wadda aka kai wa hari kwanakin baya. Daga shekarun 1975 zuwa 80, daga nan kuma sai na wuce Kwalejin Kimiyya da kere-kere ta Bauchi, sai Kwalejin NTA da ke Jos, sannan da na zo nan Amurka na yi karatu a Kwalejin Prince Geoge Community College, sai kuma Jami’ar Mary Washington.
Aminiya: Wadannan makarantu a wadanne shekaru aka yi su?
Ibrahim Alfa: Na yi Kwalejin NTA, Jos daga 1989 zuwa 1990, mu ne muka fara karatun samun takardar shaidar diploma a kwalejin, wadda ake kira Profesional Diploma on Broadcast Journalism da na Tb Production da na Engineering, sa’ilin da NTA ta bullo da wannan kwas mu ne aji na farko da muka fara zuwa. Kafi nan na yi Kwalejin Kimiyya ta Bauchi daga 1980-1982. Kuma har na fara karatun aikin lauya a Jami’ar Ahamdu Bello da ke Zariya amma saboda sha’awar wannan aikin na jarida sai na bari na dawo cikin aikin jarida wanda tun ina yaro yake cikin zuciyata.
Aminiya: Yaushe ka fara aikin jarida?
Ibrahim Alfa: Aikin jarida na fara shi tun 1983 a gidan talabijin na Bauchi, kamar yadda na fada maka na fara karatun lauya a Jami’ar ABU, a lokacin na hadu da wani fitaccen dan jarida wanda ya yi suna a wato Abdulkadir Adamu Azare (Allah Ya jikansa da rahama), ya ce mini ana daukar ma’aikata a gidan talabijin na Bauchi, sai na ce bari in je in gwada sa’a ta. Lokacin Yaya Abubakar ne Janar Manaja sai ya ce a je a gwada ni, aka je aka ba ni wasu tulin takardun labarai na Turanci aka ce in fassara su zuwa Hausa, na zauna tunda safe har zuwa dare ina abu guda, sai da na fasarre su kaf aka kai wa Yaya Abubakar ya ce kai-kai-kai. Ya ce duk inda nake son na yi karatu a duniyar nan zai tura ni don haka in zo in kama wannan aiki. A 1983 aka yi haka, to sai dai a lokacin iyayena suna son in yi makaranta ne, shi kuma Yaya Abubakar yana son in yi aikin talabijin. To haka dai ina so, ba na so na fara aiki, a lokacin ne kuma aka debo wasu abokan aikinmu aka kawo su nan Amurka karatu kamar su Aliyu Modibbo, tsohon Ministan Babban Birnin Tarayya, Abuja. Yaya Abubakar ne ya toro su, domin daga gidan talabijin na Bauchi ya tafi Amurka, sai dai ni ban samu zuwa a wannan lokaci ba, hakan kuma ya faru ne saboda yadda abubuwan siyasar kasar tamu suka kasance, domin an yanke daga kammu. To a haka na ci gaba da aikina a gidan talabijin na Baucih. Ina cikin wannan aikin sai aka tura mu kwas a Cibiyar Nazarin Harsuna da ke Jami’ar Bayero, to a wannan kwas ne na taka rawar gani domin har kyauta aka ba ni, bayan nan kuma sai aka sake tura ni Kwalejin Talabijin domin na karo karatu.
Aminiya: Shekaru nawa ka yi kana aiki a gidan talabijin na Bauchi?
Ibrahim Alfa: Na yi shekara bakwai kafin in taho nan Sashin Hausa na Muryar Amurka. Na taho nan a 1991, kuma na yi jarrabawar zuwa nan ne lokacin da nake karatu a Kwaeljin Talabijin din, a lokacin da muka yi wannan jarrabawa, Mista Koni Stephen ne Shugaban Sashin Hausa na wannan gidan rediyo, to amma kafin in zo Stebe Lukas ya zama shugaban sashin. Su Stebe sun zo Najeriya sun same ni har a kwalejin talabijin din ya ce mini ni ne na ci jarrabawar da aka yi kuma ya yi alkawarin wanda ya zo na farko ne kawai zai dauka sai dai idan mutumin ne ya ce bai so. Kuma ni ne na zo na farko don haka zabi ya rage gare ni idan ina sha’awa, to sai in shirya. Nan take na ce masa ina sha’awa tunda abin da ya sa na yi wannan jarrabawa ke nan.
Aminiya: Malam Ibrahim, ka yi aikin talabijin ne kafin ka fada rediyo, to wane bambanci ke tsakanin aikin talabijin da rediyo?
Ibrahim Alfa: Akwai bambanci kwarai da gaske, babban bambancin shi ne, shi talabijin kamar kana nuna wa mutum hoto ne. Ko a aikin jarida abin da za a koyar da kai ke nan, mutum yana ganin hoto ba za ka yi masa dogon bayani ba kamar rediyo. Domin yawancin abubuwa mutum yana gani, amma shi rediyo dole sai ka yi wa mutum bayani dalla-dalla ta yadda zai gane, kuma za ka yi ne cikin kalmomi masu sauki ba wai ka fadi wani abu wanda za ka bar mutum a can baya yana tunanin mene ne ma’anar wannan abin da ka fadi can baya ba. Don haka a rediyo akwai zaben kalmomi masu saukin fahinta ga mai saurare, babban bambancin talabijin da rediyo ke nan.
Aminiya: To yaya ka ga bambancin aikin jarida a Najeriya da nan Amurka?
Ibrahim Alfa: To na farko dai aiki a nan yana da sauki matuka, domin kana da walwalar ka yi aikinka tsakani da Allah ba wata tsangwama, muddin za ka yi shi daidai to ba wanda zai takura maka ya ce don me ka yi haka maimakon kaza, ba kamar gida Najeriya ba. Domin zan iya tunawa a gida Najeriya, an taba samun wani tashin hankali sai aka tura mu dauko labarin lokacin Gombe tana hade da Bauchi, akwai abokin aikinmu Alhaji Sani Mohammed wanda yake ofishin Jakadancin Amurka yanzu shi aka tura ya je ya dauko labarin nan a kan mutanen da aka kashe wajen tashin hankalin, amma sai aka zo ana tuhumarsa har ma kamar ana so a kore shi daga aiki. Ana cewa wa ya ce ya fada duk da abu ne da ya gani da idonsa. Ka ga daya daga cikin irin bambanci da ke akwai ke nan. Sai kuma batun kayan aiki, a nan duk kayan aikin da kake so in dai zai inganta aikinka, to za ka same shi ba tare da matsala ba.
Aminiya: To ina maganar albashi da jin dadin ma’aikaci?
Ibrahim Alfa: Albashin da ake biya a nan ba za ka kwatanta shi da wanda ake biya a Najeriya ba. Nan ana biyanka albashi ne gwargwadon yadda zai iya daukar dawainiyarka. Ka san rayuwa a nan tana da tsada sosai, to amma duk da haka za ka iya cin abinci ka yi sutura da kuma inda za ka kwana, duk ana la’akari da wadannan, amma kuma idan ka ce za ka kwatanta abin da ake ba ka da kudin Najeriya sai ka ga cewa ka yi ba daidai ba, saboda tsadar rayuwa a nan ba haka take a Najeriya ba.
Wajen biyan albashi a kan kari kuwa, tunda na zo Muryar Amurka ba a taba yin jinkirin minti daya wajen biyan albashi ba. Misali idan za a biya ka albashi ranar Juma’a, to karfe 12:01 na dare a ranar Alhamis idan ka duba za ka samu sanarwa daga bankinka cewa kudin albashinka ya shiga asusunka.
Aminiya: To, maganar sauran hakkokinka na aiki fa?
Ibrahim Alfa: Take ake ba ka hakkinka, duk abin da yake naka ne da ya shafi aikinka ba wanda zai take maka hakki a kansa, duk girman mutum a nan in kana aiki da shi ba zai iya take maka hakkinka ba. Daga kan darakta na bOA har zuwa kasa, ba wanda ya isa ya take maka hakki.
Aminiya: Wani abu a gida Najeriya da ya yi kaurin suna a aikin jarida shi ne karban abin hasafi a nan yaya batun yake?
Ibrahim Alfa: A nan idan ka karbi irin wannan abin hasafi yana iya zama sanadin barinka aiki kwata-kwata, idan aka tabbatar ka amsa sunanka korarre, maganar aiki da kai ya kare.
Aminiya: Me ke burge ka a cikin wannan aiki kuma me ke ba ka haushi?
Ibrahim Alfa: Babban abin da yake burge ni game da wannan aiki na jarida shi ne yadda idan mutum ya dage ya kuma yi aikinsa da gaskiya, zai iya taimakon rayuwar miliyoyin jama’a. Ga kuma huldar zumunci da muke kullawa da dubban masu sauraro, wasunsu ma mun zamo kamar ’yan uwa. Abin da ba ya burge ni a wannan aikin shi ne yadda wasunmu suke amfani da wannan dama da Allah Ya ba su wajen kyautata wa kawunansu kawai, tare da aikata abubuwan da ka iya haddasa fitina. Akwai ’yan jarida da dama wadanda babu abin da suka sanya a gaba sai son kai da neman fifita ra’ayoyinsu ko akidojinsu, maimakon na al’umma ko kasarsu.
Aminiya: Mece ce shawararka ga ’yan jarida musamman na gida Najeriya?
Ibrahim Alfa: Shawarata ita ce a yi aiki da gaskiya kuma tsakani da Allah, domin shi dan jarida yana da matukar muhimmaci wajen tafiyar da mulkin dimokuradiyya da kare hakkin dan Adam tare da tabbatar da abubuwa suna gudana yadda suka kamata. Kuma ya kamata ’yan jarida su fitar da kwadayi yayin gudanar da aikinsu, su daina karkatar da labarai domin cimma wani buri ko wani abu na son rai. Wannan ba zai amfane mu ba, a yi aiki ta yadda za a gina kasa ta yadda mutane za su amfana. Kada su manta cewa su kamar alkalan tabbatar da cewa gwamnati da aikinta na tafiya yadda ya kamata domin hakki ne da ya rataya a wuyan kowane dan jarida ya hukuma tana aikinta yadda ya kamata wato tana aiki da doka. Kuma dan jarida ya tabbatar bai yi wani abu da zai tada fitina a cikin kasa ba, kamar yadda muke gani ana fitintinu ana juya labarai ta yadda bai kamata ba, shawarata ke nan ga abokan aikina na Najeriya.
Aminiya: Za ka bari ’ya’yanka su yi wannan aiki?
Ibrahim Alfa: Batun ’ya’yana duk mai son aikin jarida a cikinsu, zan karfafa masa gwiwar ya yi, domin ta hanyar wannan aiki idan suka rike da gaskiya, za su iya bayar da gudunmawa mai yawa wajen yakar zamba da talauci da tabbatar da mulkin kwarai a duniya ba Najeriya kawai ba.