Sha’awar likitanci ta sa na yi wa bishiyoyi allura ina karama – Dokta Yushral Kalli

Hajiya Yushral Kali yar fitacciyar marubuciya ce, Hajiya Zainab Alkali;Tana daya daga cikin fitattun mata masu rubuta littaffai a Nijeriya. Yushural ta yi aiki a fanin likitanci da dama,  bayan haka, sai ta bude nata asibitin a birnin tarayya Abuja , don bayar da tata gudunmuwar ga al’umma. Ta yi hira da Zinariya, a inda […]

Sha’awar likitanci ta sa na yi wa bishiyoyi allura ina karama – Dokta Yushral Kalli

????????????????????????????????????

Hajiya Yushral Kali yar fitacciyar marubuciya ce, Hajiya Zainab Alkali;Tana daya daga cikin fitattun mata masu rubuta littaffai a Nijeriya. Yushural ta yi aiki a fanin likitanci da dama,  bayan haka, sai ta bude nata asibitin a birnin tarayya Abuja , don bayar da tata gudunmuwar ga al’umma. Ta yi hira da Zinariya, a inda ta ba mu labarin rayuwarta a matsayinta na uwargida da uwa da likitar yara da kuma Shugabar taimaka wa marasa lafiya a wata kungiya.

Dokta Yushral Kalli

Tarihinta
Sunana Yushral Kali Hamza, ni cikakkiyar likitar yara ce, kuma ina taimaka wa jama’a da dama ta harkar kula da lafiya. Na yi  karatun frimare na a  Firamare a makarantar  da ke Jami’ar Maiduguri a Jihar Borno. Mahaifina da mahaifiyata duk Farfesoshi ne a fanin karatu. Daga nan sai na yi karatun Sakandare a Kwalejin ’Yan mata ta Gwamnatin Tarayya ta “FGGC” da ke Yola, kuma na kammala karatun Sakandare a shekarar 1989. A shakara ta 1991, na halrci Jami’ar Maiduguri, inda na karanci  likitanci na kuma kammala a shekarar 1998. Bayan haka, na je asibitin Murtala Muhammad da ke Kano a inda na je gwajin ilimin da na samu a matsayina na likita. Daga nan na sami aiki a asibitin. Kuma na yi aiki na shekaru da dama da su. Daga bisani na yi aiki a manyan asibitocin yara da dama a Kano. Bayan shekaru 10, sannan na koma nawa aikin likitancin ba tare da wata kungiya ba.
Na yi aiki a wurare da dama wadanda suka hada da kungiyar harkar lafiya da Jami’ar New York RCRA. Na yi aiki da makarantar harkokin likitanci ta London, kuma ina cikin kungiyar Kwalejin kwararrun masu kula da lafiyar kananan yara da ke  Afrika ta Yamma . Sannan na samu babban digiri na a  fannin kula da lafiyar al’umma daga Jami’ar Liberpool.
Na yi aure, ina da ’ya’ya uku. A yanzu haka, ni ce babbar daraktar harkar lafiya a asibitin kula da yara (child care clinic).

Son da nake yi wa aikina
Aikin likitanci aiki ne na taimaka wa jama’a. Amma ina ganin aikin kamar gamo ne . domin a duk lokacin da marasa lafiya suka zo wajena na kan yi hakuri da su, kuma ban cika damuwa da cututtukansu ba. Saboda kowa yana da mahimmanci a rayuwa.  Na saba da mafi yawansu. Kula da marasa lafiya na koyar da ni aikina. Kowa yana da labarin fadi, amma don mutum ya ce min kanshi na ciwo ba shi zai sa na rubuta masa Panadol ba, sai dai na so na ji dalilin da ya janyo ciwon kan. A gaskiya ina son aikina sosai.

Abin da ba zan manta da shi ba a lokacin da nake karama
Kamar yadda na fada a baya iyayena duk farfesoshi ne. Kuma mahaifiyata marubuciya ce a Jami’a. Ba zan manta ba, takan yi rubutu da  keken rubutu, wato “typewriter,” kuma da yatsa daya take rubutun a hakan ta rubuta littafinta na farko. A hakan nake karanta wasu abubuwan da take rubutawa. Abin yana burge ni idan ina karantawa sai na ce mahaifiyata ce mai wannan rubutu. Gaskiya hakan na cikin abin da ba zan manta da shi ba.
Ba kuma zan manta da yadda na yi wasa da kannena ba. Mahaifina yakan saya min kayan aikin likita na yara a lokacin da nake karama. Na kan yi wa su bishiyoyi allura. Kuma na kan bata gida da kwabe-kwaben rowan launukan da aka saya min na makaranta. Kuma ina son karatu sosai. Nagode wa iyayena.

Shakuwata da mahaifiyata
Gaskiya na shaku da mahaifiyata. Kuma a kullum sai mun yi waya. Ko kwanakin baya da na yi tafiya don rashin lafiya, mun je tare da ita. A gaskiya mun shaku sosai abun sha’awa. Ba abin da zan iya cewa sai dai na gode mata. Kuma na koyi harkokin rayuwa da dama a wajenta, musaman dabarun tafiyartar da aikina. Mahaifiyata ita ce abar begena.
Nakan yi aiki tun safe har yamma. Ina ganin a wajenta na koyi wannan. Duk tsufarta ta kan je jihohi daban-daban don ta koyar balle ni.

Shawara daga mahaifiyata
Mahaifiyata mutum ce mai son jama’a, don haka takan ba mu shawara a kan cewa kada mu raina kowa duk talaucinsa. Na koyi hakan kuma daga gareta. Domin ko a wajen aiki na kan yi shawara da ma’aikatana. Yin hakan na daga sababin ci gabana a wajen gudanar da aikina. Irin wannan halayyar ta koyar da ni da kuma mahaifina. Shi ma ya taimaka min a harkar tafiyartar da rayuwata.

Yadda nake hada aikin asibiti da na gida
Ba karamin aiki bane ka kasance mai aikin asibiti. Zaka aiki tun safe sannan sai da yamma zaka dawo. Alhamdulillah! ‘yayana sun girma yanzu. Kuma abin yazo min da sauki don tun ban zama kwararriyar likita ba na haifesu. Nagode wa Allah da y a bani ‘yaya na gari da miji mai taimaka min.
Bazan manta ba a lokacin da nake daliba ina koyan aiki a fanin mata masu haihuwa, a lokacin ina da ‘ya a kullum sai an kawota ta sha mama sannan sai a mayar da ita. Dole ne mu jure wasu ababen.
A kowane aiki, sa kai ne. Domin sai ka yi niyyar yin aikin kafin ka sami nasara har ma ga ‘yayanka.
A lokacin da nake aiki a asibitin Murtala Muhammad ni kadai ce mace kuma nice shugabar wani bangare a asibitin kuma nice karamar cikinsu.

Nasarata
Na sami nasarori da dama a fannin aikina. Ba zan manta ba a lokacin da aka faro gano cutar kanjamau mutane da dama ba su cika son kulawa da marasa lafiyar ba, kuma a sanadin hakan, muka rasa rayukansu. Saboda babu maganin kare cutar. Sai da kungiyoyin taimaka wa harkokin kasa suka zo da kudade, domin taimaka wa masu dauke da wadannan cututtukan. Mutane da dama ba su so ba. Amma ina cikin wadanda suka bada goyon baya akan  a taimaka wa marasa lafiya. A hakan kuma muka bude asibitinmu “Family care center” muka taimaka musu muka kuma ci nasara.
Mun kuma taimaka wa mata masu juna biyu. Muna kokarin samun na’urorin aiki don kare lafiyar mata, saboda adaina fita kasashen waje don neman magani.

Farin cikin zama uwa
Ina da ‘ya’ya uku; maza biyu da mace daya. Na haifi dana na farko a lokacin da nake karatun likita. A gaskiya ba sauki; ina gida kuma mahaifiyata na kulawa da ni. A hakan dai na dage da kulawa da aikin gida da kuma karatu.
Ba zan manta ba akwai yar aiki da na taba dauko wa yara, domin ta taya ni raino.  Na kuma sanyata a makaranta. Ta yi karatun difloma kuma yanzu ta kusa hada digrinta. A gaskiya ta taimaka mini sosai.
A matsayina na likita, na kan fadi ababe da na koya a yau ba don na karanci likitanci ba ne, sai don zamana uwa, don haka ne idan ina yi wa uwaye nasiha a asibiti, na gaya musu ne ta yadda nima na tafiyar da nawa.

Yadda na hadu da maigida
Na hadu da maigida na ne a lokacin da aka kwantar da ni a asibiti. Mahaifiyata na karatun zama Dokta a fanin rubuce-rubuce a Jami’ar Bayero ta Kano. Da na je gaisheta sai aka rikeni a asibiti. A nan muka hadu da shi. Ina fama da ciwon kafa, amma a hakan yaso ni don haka nake sonsa sosai.

Kyauta daga maigidana
Babbar kyauta da na samu a wajensa shi ne, kyautar ‘yancin kai da ya ba ni. Ya kan tsaya min a duk inda ya kamata, kuma yana barina na yi aikina ba tare da takura ba. Ina mai gode masa a kodayaushe.

Inda nafi sha’awar zuwa hutu
Ina son tafiye-tafiye. Kuma na ziyarci kasashe da dama ni da maigidana a wannan shekarar. Mun kuma ziyarci kasashe kamar su Amurka da Landan.
Bara mun ziyarci wani wuri mai suna ‘bent’ wurin yana saman babban dutse ne, akwai wani fitaccen mai zane-zane ana ce da shi ‘Mackuies’ ya kan je saman babban dutsen don ya sami abin da zai burge shi ko ya zana.
Mutanen garin ba su yin Turanci. Kuma garin kauye ne. mun je mun wataya kuma mutanen garin suna da kirki.
Ina kuma sha’awar zuwa kasar Tanzaniya a duk lokacin da na samu hutu, saboda kyawun gurin. Amma ina sha’awar ziyartar Greece a tafiyar da zan yi bana.
Abubuwan da nake so a tuna ni da shi.
Ina son a tuna ni a matsayin macen da ke sha’awar taimaka wa mutane don su samu ci gaba. Ina son kuma a tuna ni a matsayin macen da ta canza rayuwar jama’a ta hanya mai kyau. Kuma da nayi iya kokarina don samar wa mutanen kasata lafiyar jiki.  

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya

Fitaccen ɗan kasuwar Kebbi, BLB ya rasu yana da shekara 54

Zaɓen Ondo: Ɗan takarar PDP ya garzaya kotu

Sarakunan gargajiya ba sa tsoron gwamnoni — Sarkin Musulmi