Sha’awar zama ‘yar jarida ta sa na shiga makaranta -Maryam mara hannuwa

Wata budurwa da aka haife ta babu hannuwa duka biyu mai suna Maryam Umar, da yanzu ta kai kimanin shekaru 20 ta bayyana cewa shawa’ar ta zama mai karanta labarai a talabijin ko zama Akanta ne ya sa ta bar yin bara ta sanya kanta a makaranta don ta dogara da kanta. Maryam Umar, ta […]

Sha’awar zama ‘yar jarida ta sa na shiga makaranta -Maryam mara hannuwa

Wata budurwa da aka haife ta babu hannuwa duka biyu mai suna Maryam Umar, da yanzu ta kai kimanin shekaru 20 ta bayyana cewa shawa’ar ta zama mai karanta labarai a talabijin ko zama Akanta ne ya sa ta bar yin bara ta sanya kanta a makaranta don ta dogara da kanta.

Maryam Umar, ta nemi masu hannu da shuni da su taimaka mata domin ta ci gaba da karatunta domin ta gaji da yin bara, saboda bara ba sana’ar da za ta dogara da ita ba ne a rayuwa.
Ta ce rashin hannuwa bai sa ta mayar da bara sana’a ba, kodayake tana yin barar tun tana karama amma yanzu da girma ya fara kama ta tana ganin bai kamata ta ci gaba da yin bara ba, gara ta shiga makaranta don ta yi ilimi don ta samu hanyar dogaro da kanta.
Maryar Umar, ta ce yanzu haka ta shiga makarantar firamare ta Jewel Academy da ke unguwar BCJ a Gombe inda take aji hudu kuma duk rubutun da ake yi da kafa take yin nata, saboda rashin hannu, kuma ba ta taba samun wata tsangwama daga wajen sauran daliban ajinsu ko na makarantarsu ba.
Ta bayyana cewa, ‘’a baya kamfanin taliyar Indomie sun dauke ni suka tafi da ni jihar Legas suka yi wani shiri da ni, inda hakan ya sa suke daukar nauyin karatuna shekaru uku da suka wuce, amma yanzu sai suka fara janyewa, shi yasa nake neman tallafin jama’a wajen ganin karatuna bai tsaya ba, don iyayena suna zaune a wani kauye ne a karamar hukumar Kaltungo kuma ba su da karfi. Yanzu haka ina zaune a wurin wani bawan Allah a garin Gombe domin ci gaba da karatuna.’’
Maryam ta ci gaba da cewa, kafin wannan lokacin tana iya biyan rabin kudin makarantar ta idan ta yi
bara, wani bawan Allah kuma ya kan biya mata rabi, amma ta ce ita bara ya ishe ta hakan nan shi ya sa take son a agaza mata.
Ta ce, ‘’idan na gama firamare zan wuce sakandare har gaba da sakandare don in zama ‘yar jarida mai karanta labarai a gidan Talabijin ko in zama akanta, saboda ina sha’awar zama daya daga cikin wadannan ma’aikatan, saboda aikin su yana burge ni.’’
“Ina son in zama mamba a kungiyar nakasassu ta jihar Gombe ko zan rika samu abubuwa da sauki, amma da na tuntubi shugaban kungiyar sai na ga yana yi mini hanya-hanya, sai na hakura.” Inji Maryam.
Maryam ta kara da cewa, duk da ba ta da hannuwa ita take yi wa kanta wanki da wanka da girki da kwalliya, hatta gugan kayanata ita take yi da kanta, idan ta yi wanki sai ta nemi wani ya yi mata shanya.
‘’Ina iya yin shara da kafafuwana, ina kuma iya yin wanke-wanke, kai wani lokaci idan na ga zan makara a makaranta ni nake dafa wa kaina shayi in sha in tafi.
Da wakilinmu ya duba littafin makarantar Maryam ya ga yadda take yin zane-zane irin wanda ake sa yara ‘yan makaranta suke yi, har ta zana kwamfuta da sauran nau’o’in zane.
Maryam ta nemi gwamnati ta kawo mata dauki kamar yadda ake taimaka wa jama’a da sauran nakasassu a jihar Gombe, musammam ma da yake uwargidan gwamna ta fito da wani shiri da ke koya wa mata sana’a (HAWEF).