Shaci-fadin Gwamnoni

Assalamu alaikum, Editan jaridar Aminiya. Don Allah ba ni dama in yi tsokaci kan shaci- fadin kungiyar Gwmanonin Najriya dangane da cewa, ba za su iya ci gaba da biyan mafi karancin albashi na Naira 18,000, wanda Gwamna AbdulAziz Yari na Jihar Zamfara ya fito yana shaida wa duniya cewa, lallai ba za su iya […]

Shaci-fadin Gwamnoni
Shaci-fadin Gwamnoni

Assalamu alaikum, Editan jaridar Aminiya. Don Allah ba ni dama in yi tsokaci kan shaci- fadin kungiyar Gwmanonin Najriya dangane da cewa, ba za su iya ci gaba da biyan mafi karancin albashi na Naira 18,000, wanda Gwamna AbdulAziz Yari na Jihar Zamfara ya fito yana shaida wa duniya cewa, lallai ba za su iya biyan wadannan kudin ba, Dama ai biri ya yi kama da mutum kuma mu al’ummar Jihar Zamfara ba mu yi mamakin hakan ba.
Don wallahi har yanzu a Jihar Zamfara akwai ma’aikatan da ake biya Naira dubu 7 a matsayin albashi, musamman ma’aikatan kananan hukumomi da malamman Firamare. Don haka muna kira ga Shugaba Muhammadu Buhari akan cewa, ya zartar da dokar biyan albashi na Naira dubu 50, sannan duk gwamnan da ya ki biyayya ga wannan doka a sa ya yi murabus daga kan mukaminsa.