Shafaffu da mai a gwamnatin Jonathan
Idan an tashi yi wa mata kirari ana cewa da su: “Mata iyayen giji, idan ba ku ba gida, idan kun yi yawa gida ya baci.” Akwai wanda zai musanta wannan batu idan aka kwatanta shi da abin da ke faruwa a fadar gwamnatin Shugaba Jonathan? Yanzu dai yawan ministocin da ke cikin gwamnatinsa ya […]
Idan an tashi yi wa mata kirari ana cewa da su: “Mata iyayen giji, idan ba ku ba gida, idan kun yi yawa gida ya baci.” Akwai wanda zai musanta wannan batu idan aka kwatanta shi da abin da ke faruwa a fadar gwamnatin Shugaba Jonathan? Yanzu dai yawan ministocin da ke cikin gwamnatinsa ya kai sulusin yawan ministoci maza, kuma a yanzu mata na hankoron ganin su da maza sun yi kan-kan-kan ba ma a sha’anin mulki ba, har ma a harkar gadin dare a kasuwanni da shagunan manyan titunan fitattun birane, domin suna cewa duk abin da maza suka yi su ma za su iya yi.
To amma da yake yanzu yawan mata ya karu a cikin Majalisar Ministoci kamar yadda Shugaba Jonathan ya yi alkawari a yakinsa na neman zabe a 2011 ana iya cewa ke nan hakan ya zame wa kasar alheri ne, ko kuma matsalar da ke wahalar da kowa da kowa? Idan hakan alheri ne to me ya sa ma’aikatun da ministoci mata ke shugabanta ba su da wani kumari kamar na wadanda mazaje ke jagoranta?
Arzikin kasar nan ya tsumbure, jama’a sun shiga cikin kuncin rayuwa da rashin walwala ba, domin komai ba kuwa sai domin ministar da ke shugabancin ma’aikatar da ke samar da arzikin da ke tallabar ayyukan alherin da ake yi don inganta halayyar zamantakewar jama’a mace ce, kuma ‘yar kabilar Shugaba Jonathan. Haka nan kuma ma’aikatar da ke sarrafa kudaden da aka samu daga wancan arzikin man fetur, wata mace ce ke kasafta su yadda ta ga dama, ita ma tana da alaka ta jinsi da uban kasa. Sauran muhimman ma’aikatun, musamman ma na kula da zirga-zirgan jiragen sama da kasuwar hannayen jari duk suna karkashin mata ne, kuma wadanda suka fito daga shiyya guda da Shugaban da suke sanya shi aikata abin da suke sha’awa, su ne kuma ke takura shi har ta kai ba abin da yake iya tabukawa.
Akwai wasu matan kuma da ba shiyyarsu daya da maigida ba, amma su ma kamar wadancan manyan matan suke. Ko a birnin tarayya ma akwai, Misis Jimoke Akinjide, wacce ta fi mai abu iko. karamar minista ce ita, amma oganta ba shi da katabus sai abin da ta ayyana ne kadai yake zartarwa. Harkkokin dangantakar kasar nan kacokan na hannun Misis biola Onwuliri, wata ‘yar koren Yahuu da Nasara, ta kanta ne ake bi a sayar da mutuncin kasar nan. Sa’annan kuma uwa-uba, ga mai dakin babban maigida, mace guda tamkar da goma. Ita ce ke rike da akalar maigidanta sai inda ta karkata shi, kamar wani zololon rakumi. To wadannan su ne matan da suka fi karfin Shugaba Jonathan, sun kuma rigaya sun kame kurwar gwamnati, sun fi karfin kowa, ba ruwansu da da’a ko ka’ida, son zuciyarsu shi ne umurnin duk wani mai rike da madafan iko, shi kuma shugaban kasa zaman lafiyarsa biye ma ra’ayin minstoci mata.
Sun rigaya sun zame wa Shugaban kasa karfen kafa, suna ta aikata masha’ar son ransu da dukiyar talakawa, ba mai hanawa.
An gano cewa daya daga cikin wadanan matan, Ministar zirga-zirgar jiragen Sama, Gimbiya Stella Oduah ta yi sama da fadi da dukiyar talakawa har Naira miliyan 255 don sayen wasu motocin gagari, wanda harsashi bai iya huda su, ba tare da bin ka’idajojin yin amfani da dukiyar jama’a wajen sayen kayayyakin da za a yi masu hidima da su ba. Baicin haka nan kuma ba domin jama’an ne aka saye su ba, sai dai don Gimbiya Odua ta kece raini da su ne, ta nuna ta isa, ta buwaya, ba kuma yadda aka iya da ita.
Wannan al’amari ya tayar da kura ainun, talakawa sun yi ta surutu, ganin yadda aka yi amfani da dukiyarsu ta hanyar da ba ta kamata ba, amma sai Ubangidan waccan ministar, Shugaba Jonathan ya yi biris, ko oho da zarge-zargen da aka yi mata sa’ilin da ‘yan kabilarta suka cika duniya da yare cewa sharri aka yi mata, a kuma bi ta kanta don shafa wa Shugaba Jonathan kashin kaji, a hana shi sake tsayawa takarar shugabancin kasa. Dalili ke nan da ya ki hanzarta hankada keyarta zuwa kauyensu, tun da dai ga hujjoji nan da ba mai iya muzantawa. Duk da cewa ya tuhume ta don ta bayyana abin da ta sani game da sayen motoci biyun, amma bai dauki mataki kan amsar da ta bayar ba, wacce a ciki ta kasa nuna wata madogara ko wani dalilin da ya sa ta aikata haka. To don me zai bata lokaci wajen kare wacce aka samu da laifi dumu-dumu, har yana kafa kwamitin bincike don a kara batar da dukiyar talakawa? An dai ce son zuciya bacinta, kuma idan Shugaba Jonathan ya ci gaba da biye shawarar matan da ya shafe da mai, to za su kai shi, su baro a banza.