Shafin Instagram ya daina aiki a Rasha

Hukumomin kasar dai na zargin kamfanin da na zargin shafin da iza wutar rikici

Shafin Instagram ya daina aiki a Rasha

Instagram

Shafin Instagram ya daina aiki kwata-kwata a Rasha bayan kasar ta zargi kamfanin Meta, mamallakin shafukan Instagram da Facebook da WhatsApp, da iza wutar rikicinta da Ukraine.

Hukumomin kasar dai na zargin kamfanin da kiran mutane su musguna wa ’yan Rashar, ciki har da sojoji a shafukansu.

Matakin dai na zuwa ne bayan kasar ta toshe shafukan Facebook da Twitter a farkon wannan watan, a wani yunkuri na tantance nau’in bayanan da ’yan kasar za su samu daga shafukan kan mamayar Ukraine.

Sunan shafin na Instagram dai ya bayyana a jerin sunayen manhajojin intanet din da aka hana amfani da su a kasar, wanda hukumar kula da kafafen yada labarai ta kasar mai suna Roskomnadzor ta yi.

A wani labarin kuma, hukumomin kasar Ukraine sun ce daga fara yakin zuwa yanzu, an kashe sama da mutum 2,500 a birnin Mariupol kawai.

Mai ba Shugaban Kasar Ukraine shawara,  Oleksiy Arestovych, ne ya bayyana hakan a wani jawabinsa da aka watsa ta gidan talabijin.

Ya ce sun tattara alkaluman ne daga hukumomin birnin, sannan ya zargi Rasha da hana masu ba da agaji kai wa ga mutanen birnin wanda ta yi wa kawanya.

Sai dai Rasha ta musanta zargin, inda ta ce hare-harenta ba sa fakon fararen hula.