Shagari jagora ne abin koyi – Jonathan

Shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan ya jagoranci dukkan tsofaffin shugabannin kasar nan sun taya tsohon Shugaban kasa Alhaji Shehu Usman Aliyu Shagari murnar cika shekara 90 a duniya. A shekaranjiya Laraba ne Alhaji Shehu Shagari ya gudanar da bikin cika shekara 90 a duniya a gidansa da ke Unguwar Sama a Sakkwato Birnin Shehu.Tsofaffin shugabannin […]

Shagari jagora ne abin koyi – Jonathan
Shagari jagora ne abin koyi – Jonathan

Shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan ya jagoranci dukkan tsofaffin shugabannin kasar nan sun taya tsohon Shugaban kasa Alhaji Shehu Usman Aliyu Shagari murnar cika shekara 90 a duniya.

A shekaranjiya Laraba ne Alhaji Shehu Shagari ya gudanar da bikin cika shekara 90 a duniya a gidansa da ke Unguwar Sama a Sakkwato Birnin Shehu.
Tsofaffin shugabannin kasar nan hudu da suka hada da Janar Yakubu Gowon da Janar Ibrahim Babangida da Cif Ernest Shonikan da Janar Abdulsalami Abubakar da Shugaba Jonathan sun dafa wa Alhaji Shehu Shagari wajen yanka kek din cikarsa shekara 90. Tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya isa Sakkwato daga baya, yayin da tsohon Janar Muhammadu Buhari da ke Landan ya aike masa da sakon taya murna.
A wurin bikin Shugaba Jonathan ya bayyana Shagari a matsayin abin koyi da ya tsayu don ganin kasar nan ta kasance kasa daya ba tare da nuna bambancin kabila ko yanki ba, “Tun kana matashi kake kokarin ganin kasar nan ta zauna lafiya cikin hadin kai har yanzu ba ka nuna kosawa ko gajiyawa ba,” inji Jonathan.
A jawaban Yakubu Gowon da Ibrahim Babangida da Ernest Shonekan da Abdulsalami Abubakar sun ce “kasar nan tana da abin koyi daga Shagari kan tausayi da kwazo da jajircewarsa, wannan ziyara ce da tarihi ba zai mance da ita ba, na nuna farin cikinmu gare shi da Allah Ya kawo shi wannan rana mai tarihi ga kasar nan da Ya bai wa karfinsa don ci gaban tattalin arzikinta da hadin kanta.”
Janar Babangida ya ce: “Ba zan manta da Shagari ba kuma a kullum ina gode masa kan karin girman da ya yi min na zama Birgediya Janar a soja, ban da wannan damar da ya ba ni, da ban samu damar da na samu a yanzu ba, a lokacin da Shagari yake Shugaban kasa ya kamata ya cire ni daga soja don an same ni a cikin lamarin juyin mulki da dama amma ya kawar da kansa, har Allah Ya kaddare ni da jagorantar kasar nan, ina godiya ga wannan damar da ya ba ni.”
Alhaji Shehu Shagari ya gode wa dukkan mahalartar taron tare da nuna farin cikin gabatar masa da katin sanya hannu da Yakubu Gowon ya gabatar a madadin tsofaffin shugabannin kasa ciki har da Buhari da Obasanjo da ba su wurin yanka wainar ranar haihuwarsa ba.
An gabatar da addu’a ta musamman wadda Sarkin Malaman Sakkawato Alhaji Buhari Siriddawa ya jagoranta.